Ubangiji ya ce kada in tsaya takara a 2027 – Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce Allah ya ce kada ya tsaya takara a 2027.

Mista Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Makurdi lokacin da mambobin jam’iyyar People’s Democracy Party, PDP, G-14 suka kai masa ziyarar ban girma.

Mambobin G-14 dattawan jam’iyyar PDP ne a ƙananan hukumomi 14 da ke magana da harshen Tibi a Benue.

Tsohon gwamnan ya ce ba shi da wani zaɓi illa mutunta nufin Allah.

Ya yarda cewa ya kasa tuntuɓar Allah kafin ya shiga zaɓen 2023, shi ya sa ya sha kaye.

Mista Ortom ya bayyana cewa PDP ta kuduri aniyar karbe gidan gwamnatin Benue a shekarar 2027.

“Bana takara a zaɓen 2027. Na san dalilin da ya sa na faɗi zaɓe a 2023. Ban nemi zaɓin Allah ba. Jama’ata sun saya mini fom, na karɓa ba tare da neman yardar Allah ba.

“Allah ya bayyana mini komai. Ya ce in jira shi,” in ji shi.

Mista Ortom ya ci gaba da bayyana cewa, a lokacin da yake yi wa jihar hidima a matsayin gwamna, ya yi sadaukarwa mai yawa, ciki har da yin watsi da ‘yan uwa da abokan arziki a wani lokaci kan harkokin jihar.

Tsohon gwamnan ya yi alƙawarin ci gaba da marawa jam’iyyar baya, inda ya ƙara da cewa babu wani buri da ya isa ya wuce muradun jam’iyyar.

A cewarsa, bayan ya bar ofis, ya so ya tafi hutu, amma dattawan sun ƙi amincewa.

Mista Ortom ya ce babu wanda ke da hurumin wargaza babbar jam’iyyar PDP G-14, har ma da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.

“A matsayina na shugaban jam’iyyar a jihar, ba ni da ikon rusa jam’iyyar. Don haka babu wanda zai iya wargaza wannan tawaga.

“G-14 taron dattawan PDP ne a Benue. Idan wani abu ya faru, dole ne na fara sani domin ni ne shugaba,” inji shi.

A taron da ke tafe, ya ce, tuni sakatariyar ƙasa ta amince da majalisun unguwanni da na ƙananan hukumomi na Benue, inda ya ce za a gudanar da taron na jihar a ranar 3 ga watan Oktoba.

Ya ce tuni ya yi magana da Sen. Gabriel Suswam da Sanata Abba Moro, kuma sun amince su ƙarfafa haɗin gwiwa gwargwadon iyawarsu saboda suna adawa.

Shugaban jam’iyyar PDP G-14, Dr Laha Dzever, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugabancin Ortom.

Mista Dzeɓer ya ce sun sake zuwa ne suka yi alkawarin marawa shugabancinsa baya tare da yin alkawarin samar da zaman lafiya da haɗin kan jam’iyyar.

Shugaban ya bayyana cewa a siyasance dole ne a samu saɓani lokaci-lokaci, yana mai jaddada cewa rigingimun cikin gida da ake fama da su a cikin jam’iyyar za ta ƙara ƙarfi ne kawai.

Ya yaba wa Mista Ortom bisa namijin ƙoƙarin da yake yi na ganin jam’iyyar PDP ta ci gaba da kasancewa babbar jam’iyya mai haɗin kai a jihar.

Dangane da rugujewarsu, Dzeɓer ya ce babu wanda ya zaɓi ƙungiyar da aka kafa a shekarar 2015 a ƙoƙarinmu na ganin jam’iyyar bata ruguje ba bayan ta faɗi zaɓe.

“Mutumin da zai iya tarwatsa mu shi ne shugaban jam’iyyar a jihar, kuma shi ne Cif Ortom. Ku kaɗai za ku iya wargaza abin da kuka kafa,” inji shi.