Uwa: Makarantar farko ga ‘ya’yanta

Daga AISHA ASAS

Annabin rahma ya ce, “daɗin duniya na tattare da samun mace ta gari” domin da mace ta gari ce za ka samu kwanciyar hankali, za ka samu natsuwa tare da biyan buƙatun yau da kullum, ga uwa uba samun ‘ya’ya na gari.

A yau darasinmu na iyali zai karkata ne kan maza, tun daga samari da ba su yi aure ba, zuwa magidanta da ke shirin ƙarin aure. Domin dai kuskuren daga wurin ku ne ya samo asali.

Da yawa daga maza abin da suka fi kallo a matar da za su aura ba shi da tasiri a zaman nasu na aure. Duk da cewa, a kullum malamai na faɗakarwa kan irin matan da ya kamata a aura, wanda rashin bin kiran su na cutatar da kai kanka da kuma ‘ya’yan da za ku haifa, har ma ita kanta matar, tare da al’umma bakiɗaya. 

Ta yaya matar da za ka aura zata iya cutar da kai, ‘ya’yanka da ita kanta?

Mace ta gari ce ta san muhimmancin sauke haƙƙoƙin ka da ke kanta. Ita ce ta ke da ikon iya mayar ma da gidanka muhallin da ya fi kowane muhalli kawo kwanciyar hankali gare ka. 

Ita ce za ta rufa asirinka, domin ba wadda ta san ka kamar ta. Ta yi haƙuri da gazawar ka. Da waɗannan misalai kawai za ka iya ba wa kanka amsar ko zata iya cutar da kai idan ka samu saɓanin irin wannan mata.

‘Ya’yanka: bincike ya tabbatar kaso mafi rinjaye na yaran da ke lalacewa su addabi jama’a sun fito ne daga gidan da tarbiyya ta yi ƙaranci, idan za ka bi matakalan tarbiyyarsu akwai yuwar ba za ka samu uwa ta gari ba.

Duk da na san akwai waɗanda ake jarrabtawa ta ɓangaren ‘ya’ya, ta hanyar ba su gurɓatattun yara, don Allah ya jarrabta imaninsu, sai dai waɗanda ba su yi sa’ar uwa ba sun fi yawa a cikinsu.

Uwa ta gari ce za ta fara koyar da ‘ya’yanta da halayyar ta. Irin zaman da ta ke da mijinta, da mutane ne zai zama makaranta ta farko gare su. Har wa yau, uwa ta gari ce ta damu da sallar ‘ya’yanta, karatun ‘ya’yanta da kuma yadda suke mu’amalla da mutane.

Ya kai maigida ka sani, tarbiyyarka ga ‘ya’yanka ko kusa bata kai ta uwarsu ba, duk ƙoƙarin ka wurin gina ‘ya’yanka kan turba mafi daidai, idan ba ka da mace ta gari to fa ragagiya ce, don za ka dinga tubka ne, tana warwara. A taƙaice dai uwa ce makarantar farko ga ‘ya’yanta, idan kuwa ba ka nemo musu wadda za ta iya koyar da su daga kyawawa, ta hane su da mummuna ba, to tabbas ka cutatar da su, kuma ba su kaɗai ne za su koka ba har da kai kanka, da kuma al’umma, kasancewar su masu jan ragamar al’umma a gaba.

Matar: Na san za ka ce ya auro macen da ba ta gari ba zai cutar da ita. Idan har maza za su guje wa auren macen da ba ta ƙwarai ba, to matan za su rasa mazajen aure, idan kuwa hakan ta kasance, ba su da zaɓi sai na dawo wa su bi matakan zama mata na gari don su samu mai ɗaukar su. Kaga kuwa auren su da ku ke yi zai sa su tunanin ba su tare da illa, don haka ba zancen gyara gare su, kenan kun cutar da su ta hanyar hana su ganin aibun halayyar su bare har hakan ta kai su ga gyara.

Annabin rahma ya ce, “ku nema wa ‘ya’yanku uba/uwa na/ta gari.” Idan za ku yi aure, kada ku bari kyau, matsayi ko dukiya su zama dalilai mafi rinjaye a zaɓin naku, domin da-na-sani zai iya biyowa baya. Ku yi wa ‘ya’yanku adalci tun ba ku haife su ba.

Karancin uwaye na gari masu ilimin addini na cikin ummul khaba’isin ta’addanci da baɗa’llar da ta yawaita ga yaran wannan zamani. Uwa ce kaso mafi rinjaye na rayuwar ɗanta, don haka iliminta haske ne ga al’umma gabaɗaya, saboda ita ce makaranta ta farko ga ɗanta, kuma kamar yanda muka sani, “karatun ƙaramin yaro tamkar rubutu ne kan dutse,” ba abinda zai iya fitar da shi, sai dai ya ɗora wani saman sa, kuma zai yi wuya ya kasance daban da wanda aka fara gina sa kansa.