Wa kuma Isra’ila za ta kashe bayan Sinwar?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kamar yadda mu ka ambata a baya ko kuma yadda ma lamarin ya ke a Oktobar nan ta 2024 yaƙin da a ke yi kan Gaza ke cika shekara ɗaya da kuma shiga shekara ta biyu. Yayin da Isra’ila ke bayanan harin ’yan Hamas na ranar 7 ga Oktobar bara ya yi sanadiyyar kashe mutum miliyan 1200, a na ta ɓangaren Isra’ila ta kashe dubun-dubatan Falasɗinawa da ƙidayar da a ke yi yanzu sama da Falasɗinawa dubu 40 ne a ka kashe a Gaza ciki da mata da ƙananan yara. Ba a nan yaƙin ya tsaya ba, hare-haren manyan boma-bomai da Isra’ila ke yin asha ruwan tsuntsayen su daga jiragen yaƙi, sun rugurguza gine-gine a Gaza. 

A wasu lokutan ma a kan sha wuya ainun wajen tono gawawwakin waɗanda gine-ginen da su ka ruguje su ka danne. Gaskiyar magana wasu ma ƙarƙashin gine-ginen kan zama kaburburan su na farko kafin wataƙila bayan sun dudduge a gano su. Isra’ila kan ce ta na farutar ’yan Hamas ne da ta ce kan fake a yankunan da fararen hula ke zama ciki da makarantu da asibitoci. Isra’ila ta yi ta gigita Falasɗinawa ta na umurtar su, su yi gudun hijira daga arewaci zuwa kudancin Gaza. Duk da yin hakan ba su tsira daga ruwan boma-bomai ba. Za ka ga Falasɗinawa dauke da kayan su a ka su na ragaita tsakanin garuruwan yankin Gaza har ta kan kai ga su zauna a sararin subhana. Hatta can garin Rafah na kan iyakar Gaza da Masar inda dubban Falasɗinawa su ka taru ba su samu salama ba don Isra’ila ta shiga yankin da kashe-kashe ba. 

Duk Masar na cikin ƙasashen da ke jagorantar neman dakatar da yaƙin Gaza amma ba ta da kwarin guiwar buɗewa Falasɗinawa mashigar Rafah su shiga yankunan ƙasar ta don samun sararawa. Matakin kawai ma da Masar ta ɗauka shi ne cewa ba za ta amince Isra’ila ta jibge sojojin ta a kan iyakar ta ta Rafah ba. Iya maganar kenan don yanayin siyasar yaƙin ba zai sa Masar ta iya turo sojoji ko ɗaukar wani mataki mai ƙarfi kan Isra’ila ba. Wato tun yaƙin da ƙasashen Larabawa su ka yi da Isra’ila wajen 1967 ba a sake samun wata arangama ta kai tsaye tsakanin ƙasashen da Isra’ila ba. 

A yakin dai Isra’ila ta yi nasara kan ƙasashen Larabawa har ma da mamaye wasu sassa na Masar da Sham. Nazari ma ya nuna wasu ƙasashen Larabawan sun yi lako-lako ne don Isra’ila ta samu nasara da hakan zai taimakawa siyasar su a ƙasasahen duniya. Kare ɗaiɗaikun ƙasashen su ya fi mu su a’ala a kan tsayawa kan samun ‘yancin Falasɗinawa. Yo in ma Falasɗinawa duk za su kare su ƙasashen su ko gwamnatocin su, su wanzu ai ba zai zama wani abun tada jijiyar wuya ba. 

Kawai a manta da tunanin Larabawa za su iya aiki tare don muardin gwamnatocin ƙasashen su da su ka haɗa da na mulkin mulukiyya wajen neman dauwama kan karagar mulki. Sarauta dai mulki ne na gado tsakanin ’yan uwa na iyali ɗaya. Batun nan fa ba daidai ne a zargi addini ko malaman Islama da ke ƙasashen Larabawa ba. A takaice sarauta daban malamai daban duk da ba lalle a ace hanyar jirgi daban na mota daban ba a tsakanin sassan biyu a ƙasashen. Dole mu kauce yin kuɗin goro ga rashin ɗaukar matakan zahiri daga ƙasashen Larabawa. 

Duniya ta riga ta sauya tsakanin ƙasashe masu ƙarfi da marar sa ƙarfi ko masu ƙarfi da masu kare gwamnatocin ƙasashen da jagororin su ke son dauwama kan mulki. Mun ma sha maimaita cewa hatta a tsakanin Falasɗinawa akwai rabuwarkai tsakanin Hamas da gwamnatin Falasdinu mai faɗa a Ramallah.

Labarun Falasɗinu da Hezbollah a tsakanin nan:

Wani mummunan hari da Isra’ila ta kai kan wata makaranta a Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28.

Makarantar a garin Deir Al-Balah na zama wata mafakar ’yan gudun hijira da su ka kauracewa wasu sassa a sanadiyyar yaƙin da ke gudana.

Wannan yaƙin dai da yanzu ya shiga shekara ta biyu ya yi sanadiyyara kisa ga fiye da Falasɗjnawa 40,000.

A tsakiyar Beirut kuma babbar birnin Lebanon wani harin na Isra’ila ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 22.

Majiya daga gwamnatin Lebanon ta bayyana cewa harin ya auna wani jigo ne na mayaƙan Hezbollah.

Kazalika harin a cewar majiyar ma’aikatar lafiyar Lebanon ya raunata mutum 117.

Duk da ba wannan ne karo na farko da Isra’ila ke auna hari kan kudancin Beirut ba, amma wannan shi ne na 3 da Isra’ila ta kai tsakiyar birnin.

Harin samaniya da Isra’ila ta kai kan garin Aitou mai akasarin mazauna mabiya addinin Kirista a arewacin Lebanon ya yi sanadiyyar rasa ran kimanin mutum 19.

Bayanai daga ƙungiyar agajin Red Kuros sun bayyana cewa harin ya shafi wani bene mai hawa 3 da wasu da ke gudun hijira su ka kama hayar sa.

Hakanan Isra’ila ta cigaba da kai hare-hare sassan Lebanon da hakan ke ƙara sanya asarar fararen hula.

Harin ya biyo bayan wani harin da mayaƙan Hezbollah su ka kai kan wani sansanin horar da sojojin Isra’ila a Haifa inda kimanin sojojin Isra’ila 4 su ka mutu yayin da fiye da 65 su ka samu raunuka.

Babban hafsan rundunar sojan Isra’ila Janar Hezi Haleɓi ya nuna matuƙar takaici kan harin da ya ke cewa ba za su amince da irin hakan ba.

Haleɓi ya ziyarci sansanin atisayen da ke kudancin Haifa inda ya nuna juyayin sa kan waɗanda su ka mutu da kuma waɗanda su ka samu raunuka.

ƙungiyar Hezbollah ta yi gargaɗin kai hari a dukkan Isra’ila tun da sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare a ko ina a Lebanon.

Mataimakin sakataren Hezbollah Na’im ƙassem ya bayyana haka a wani faifan bidiyo da a ka ɗauke shi ya na magana ga tutar Lebanon da ta Hezbollah a gefen sa.

ƙassem ya ce jam’iyyar Hezbollah na nan a haɗe da ƙarfin ta kuma kenan ba za ta zuba ido Isra’ila na kashe-kashe a Lebanon ba.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya umurci sojojin sa kar su saurarawa Hezbollah wajen hare-hare.

Wasu ‘yan siyasar Lebanon na kira ga Firaministan Lebanon Najib Mikati da shugaban majalisa Nabih Berry su bukaci Hezbollah ta amince da tsagaita wuta.

Halin da a ke ciki Hezbollah na arangama da sojojin Isra’ila a garin Thalathine na kan iyaka da amfani da manyan bindigogi da makamai masu linzami.

Isra’ila ta baiyana cewa ta kashe shugaban ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar a wani hari da ta kai a kudancin Gaza.

Bayanai daga Isra’ila sun tabbatar da kashe Sinwar bayan duba gangar jikin da ke nuna haƙiƙa ta Sinwar ce.

An ba da labarin Sinwar ne ya shirya harin 7 ga Oktobar bara da ya yi sanadiyyar ɓarkewar wannan yaƙin da a ke yi yanzu da ya kai fiye da shekara ɗaya.

Ba bayanai na nan take daga farko daga Hamas da ke nuna mutuwar Sinwar amma dai alamu sun nuna Allah ya karɓi rayuwarsa.

In za a tuna biyo bayan harin Isra’ila da ya yi sanadiyyar kashe shugaban Hamas Isma’il Haniyeh a Tehran, ƙungiyar Hamas ta sanar da naɗa Sinwar.

Wata ɗabi’a ta Sinwar ita ce duk gwagwarmayar da Hamas ke yi, bai taɓa ficewa daga yankin Gaza ba.

A tsarin Hamas zai yi wuya a kai nan da mako ɗaya ba ta aiyana sabon shugaba ba kuma wanda mutuwa ba za ta zama fargaba a gare shi ba.

Wani harin da Isra’ila ta kai arewacin Gaza kan wata makaranta da ta koma muhallin zama ya yi sanadiyyar kashe kimanin Falasɗinawa 28 ciki da yara.

Kakakin ma’aikatar lafiya na Gaza Medhat Abbas ya tabbatar da labarin harin inda ya ce mutane sun ƙone kuma ba ma ruwan da za a kashe gobarar da ta tashi.

Kazalika gomman mutane ne a bigiren su ka samu raunuka a sanadiyyar ƙunar wuta da ta shafe su.

Isra’ila ta ce ta kai hari bigiren ne don taruwar wasu ‘yan Hamas da ta kai hari kenan don murƙushe su.

Medhat ya yi watsi da kalaman na Isra’ila ya na mai cewa harin na nuna kisan kare dangi ne daga Isra’ila.

Isra’ila ta bayyana cewa harin jirgi marar matuƙi daga ƙungiyar Hezbollah a Lebanon ya auna gidan firaminista Benjamin Netanyahu.

Harin dai ya shafi gidan da a ke cewa na Netanyahu ne a garin Caesarea amma majiyoyin Isra’ila sun ce Netanyahu da matar sa ba sa gidan a lokacin da a ka kai farmakin.

Hezbollah ta ce ta na ƙara ƙaddamar da hare-hare kan Isra’ila da ingantattun makamaki masu linzami.

An ba da labarin wani mutum daya da burbushin makami mai linzami na Hezbollah ya taɓa a garin Acre mai tashar teku cikin Isra’ila ya mutu yayin da wasu mutum 5 a Kiryat Arba su ka samu raunuka.

Isra’ila kuma ta kai wani mummunan hari da ya taɓa garin Jabalia na Gaza inda mutum 33 su ka rasa ran su.

Kammalawa;

Tsohon shugaban Amurka Doald Trump ya aza alhakin yaƙe-yaƙe a wasu sassan duniya da rashin tsarin shugaban Amurka Joe Biden.

Trump wanda shi ne ɗan takarar jam’iyyar Rifabulikan a zaɓen Amurka da a ke shirin gudanarwa a watan gobe, na magana ne kan yaƙin Gaza da kuma Yukrain.

Donald Trump ya ce in da shi ne a kujerar mulkin White House da ma ba a kai harin 7 ga Oktobar bara a cikin Isra’ila da ta kawo yaƙin da a ke yi na Gaza ba.

Trump na zantawa da wakiliyar kafar labaru ta Al-Arabiya inda ya ce da duk ba a yi asarar rayukan da a ka yi ba.

Tsohon shugaban ya ce ya na da muradin dawo da yarjejeniyar dangantakar tarihi ta Larabawa da Yahudawa wato “ABRAHAM ACCORD” don matso da sassan biyu su riƙa hulɗar diflomasiyya.

A 2020 Trump ya jagoranci ƙulla dangantakar tsakanin ƙasar Bahrain da Daular Larabawa tare da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House.