Daga AISHA ASAS
Wanka shi ne abu na farko da duniyar kwalliya ta fara shar’antawa, don haka ba kwalliyar da za ta yiwu idan babu wanka. Macen da ba ta ɗauki wanka da muhimmanci ba, tamkar ta nisanci kwalliya ta haƙiƙan.
A lokacin da ki ka zama ƙazama, ki ka sanya ƙyuya a jikinki, ki ka bijire wa wanka, to kin zama ballagaza ko da ke mai tsaftace fuska, shafe-shafe da sanya turare ce.
Abin lura dai, idan kin ƙaurace wa wanka to ki haƙura da kwalliya, domin kwalliya kan yi kyau ne bisa bin sharuɗan ta. Kuma babban jigo a sharuɗan shi ne tsafta. Wanka kuwa shi ne ya haifi ko wane nau’i na tsaftar jiki.
A wannan gaɓar zan janyo hankalin mata ƙazamai da suke da kunnen ƙashi. Domin an jima ana kira da jan kunnen mata akan tsafta. Kuma mai jan kunnen ba ya saka aya har sai ya sanyo tsafta ta jiki, kuma wanka ne ja gaba.
Duk yadda ki ke ganin ki na ɓadda kama, ma’ana ki na wanke fuska, hannu da ƙafafu (tsaka-tsami) ki sani rashin wanka zai bayyanar da kansa.
Uwargida ki na tashi da safe kin yi kalaci, kin yi aikace-aikace idan ke mai yin ce, kin yi girkin rana zuwa na dare, duk datti da ƙarnin abinci da na zufa su na tare da ke, amma ki kasa zuwa bayi ki ba wa jikinki na sa kulawa. Sai dai ki saka soso da sabulu ki wanke hannu da fuska da ƙafa ki fito. Ki cika fuska da foda da ja gira, ki baɗaɗe jiki da turare, ke nan kin caɓa ado.
To albishirin ki uwargida, wannan datti da warin da ki ke tunanin kin masa dabara kin kawar da shi yana nan ba inda ya je, kuma dama kaɗan yake nema ya fitar da kansa ba tare da kin sani ba.
Turare da ki ke amfani da shi don fin ƙarfin warin jiki ba ƙamshi yake bayar wa ba, ‘kamshiwar’. Maigida ne zai iya tabbatar da zance na, domin shi ne mai jin ƙamshin.
A daidai wannan gaɓar na ke janyo hankalin mata ka da sanyi ko ƙyuya su hana ki wanka. A ɗauki wanka da muhimmanci ko mai tsananin sanyi. Ko ba ki yi ba a ƙalla ki yi wanka sau biyu a rana, don kawar da dattin safe da ta rana kafin a kwanta.
Wannan shafin na wannan jarida mai farin jini na wannan sati ya tanadar wa uwargida, amarya, budurwa, kai har ma da bazawara tsaraba da za ta taimaka wajen kawar da datti yayin wanka, ta kuma inganta fata tare da sanya ta sheƙi tun ba a kai kan kwalliya ba.
Sabulu na ɗaya daga cikin muhimman ababe da ke inganta wanka. Kuma yana da matuƙar muhimmanci mu kula da irin sabulan da fatarmu ke buƙata, da kuma waɗanda za su taimaka wa lafiyar fatar mu da sanya ta ƙyalli.
Uwargida za ta tanadi kaya kamar haka:- Lemon tsami( amfani da lemon tsami na da buƙatar ta-ka-tsam-tsam, kasancewar ba kowacce fata ce ke marhabin da shi ba. Da wannan zan ce ki fara sanin matsayin sa a fatarki kafin ki san adadin da za ki yi amfani da shi ko barin shi), zuma, jar dilka, garin karas, sabulun pharmaderlm, kanwa, sabulun Asef. Ki daka sabulan, ki zuba kanwa daidai misali (garin ta), ki ɗauko dilka da ki ka kwaɓa da ruwan zafi ki zuba a ciki. Lemon tsami za ki matse daidai ki saka a ciki. Sai a zuba zuma a haɗe su har sai sun dunƙule da juna. Wannan sabulun zai fi aiki gurin kawar da ƙuraje na fuska, duk da cewa ya na gyara fatar jiki. Sai dai zan so uwargida ta lura da wani abu, akwai sinadarai da idan sun yi yawa za su iya cutatar da fata irin lemon tsami, don haka zai fi kyau a san yadda za a saka shi. Misali, kin sa sabulan ko wane biyu, to za ki saka rabin cokali ƙarami na kanwa. Lemon tsayi ɗaya marar girma sosai. Dilka cokali babba ɗaya. Zuma cokali huɗu.