Waɗanda ke da haƙƙin kare gwamnatina sun bari ana kushe ta – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce duk da irin nasarori da kyakkyawar gwamnatinsa ta samu amma waɗanda ya kamata su yi magana kan nasarorin da ya samu ba sa yin hakan.

Buhari, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wata liyafar karrama shi da aka gudanar a garin Owerri na jihar Imo lokacin ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai jihar.

“La’akari da lokaci da kuma albarkatu, wannan gwamnati ta yi kyakkyawan aiki. ne in faɗa saboda waɗanda ya kamata su faɗi ba su faɗi ba. Ban san dalili ba, ”inji Buhari.

Shugaban ya zargi gwamnatocin da suka shuɗe da gazawa wajen samar da ababen more rayuwa da vangaren wutar lantarki, duk kuwa da ɗimbin kuɗaɗen shigar da ake samu daga haƙo mai.

“A kan batun rashin tsaro da ‘yan fashin daji da gadar Neja ta biyu, idan ‘yan Nijeriya za su yi tunani; duk da haka, gaskiyar magana, ina zargin jiga-jigan Nijeriya da rashin zama akan matsalolin da kuma yin tunani mai zurfi game da ƙasarmu,” inji Buhari.

“Tsakanin 1999 zuwa 2015 da muka shigo, zan so mutane su duba Babban Bankin Ƙasa da kuma kamfanin mai na ƙasa NNPC.

Matsakaicin abin da ake haƙowa ya kai ganga miliyan 2 da dubu 100 a kowace rana kan farashin dala 100 kan kowace ganga.

Don haka Nijeriya tana samun riba a wannan lokaci ko wacce rana dala 100 sau yawan adadin ganga miliyan 2 da dubu 100 a waɗannan shekarun.

Sai dai kuma, ana sukar gwamnatin Buhari da taɓarɓarewar basuka, da matsananciyar taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma son zuciya wajen magance matsalar Fulani da makiyaya.

Bayanai daga ofishin kula da basuka na nuni da cewa adadin bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 41 a ƙarƙashin jagorancin Buhari.

A yayin da gwamnatin ke shirin ciyo bashin sama da Naira Tiriliyan 11 domin gudanar da kasafin kuɗin shekarar 2023, gwamnatin Buhari za ta bar wa Nijeriya bashin Naira tiriliyan 50 idan ya bar mulki a watan Mayun shekara mai zuwa.