Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta soke zaɓen fidda gwanin PDP na Gwamnan Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP na takarar gwamna a zaɓen 2023 mai zuwa.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Aminu Baffa ya yanke hukuncin ne ranar Juma’a yayin da kotu ta yanke hukunci kan ƙarar.

“Bisa hukuncin da kotun ta yanke mai shafi 109 kotun ta gamsu da ƙarar da Injiniya Ibrahim Shehu Gusau ya shigar a gabanta a kan PDP, Adamu Maina Waziri, Kanar Bala Mande, Dauda Lawal Dare da INEC kan rashin bin ƙa’ida a zaɓen gwamnan PDP da aka kammala a ƙarshen zaɓen fidda gwani a Jihar Zamfara.

“Don haka kotu na da hurumin shari’ar, kuma kotu ta yanke hukunci kan waɗanda suka shigar da ƙara,” inji alƙalin kotun.

Kotu ta soke zaɓen fidda gwani na gwamnan PDP na Jihar Zamfara, inda ta buƙaci a sake sabon zaɓen fidda gwani na gwamnan PDP.

A wata hira da manema labarai jim kaɗan bayan yanke hukuncin kotun, lauyan masu shigar da ƙara, Barista Ibrahim Ali ya bayyana cewa Babbar Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara gabanin babban zaɓen 2023 daidai da tsarin mulkin PDP da jagororinsa.

Barista Ali ya bayyana jin daɗinsa da yadda kotu ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ba tare da wani tsoro ko nuna bambanci ba.

Shi ma da yake mayar da martani kan hukuncin, mashawarcin PDP na jihar, Barista Bashir Abubakar Masama ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za su duba hukuncin da kuma ɗaukaka ƙara domin a yi adalci.

By Editor