Wa Zai Auri Ma’aikaciyar Lafiya?

Daga AMINA YUSUF ALI

Kafin mu shiga cikin bayanin ka’in-da-na’in, ya kamata ma mu sani bangaren da muke magana a kai wato ƙasar Hausa. A ƙasar Hausa da ma karatun boko ko aikin mata wani abu ne wanda har yanzu bai samu karɓuwa da hannu bi-biyu ba. Gara ma ga yara maza wasu masu ɗan sassaucin ra’ayin sun rungume shi. Amma ita mace kullum ana ganin ma kamar wani yahudanci ne ko kuma fin ƙarfin miji ne ko iyaye idan ta yi zuzzurfan ilimin boko.

Har ma ta fara aiki a ma’aikatar gwamnati ko ma’aikata mai zaman kanta. Kamar aikin koyarwa, aikin asibiti, aikin banki, aikin kamfani, aikin jarida da sauransu Idan mutum yana ji ta bakin waɗannan mata, zai ji irin tarin ƙalubalen da suke fuskanta. Musamman ma a ɓangarorin da gargajiya ta fi karfi. Yanzun nan za ka ga al’umma sun yi mata caaa! Idan ba a yi sa’a ba ma ta zama abar zargi. Amma rukunin mata ma’aikatan da nake son na yi magana a kansu, sun fi kowa fuskantar ƙalubale. Wato mata ma’aikatan lafiya. Saboda ba kowa ne yake son aurensu ba duk da ɗimbin alkhairin da suke da shi.

Wace ce ma’aikaciyar lafiya?
Ma’aikaciyar lafiya ita ce mace wacce take aiki a daya daga cikin sassan asibitocinmu domin ceto rayuka. Kama daga kan manyan likitoci mata, masu tiyata/fiɗa, likitocin haƙori, masu yin aiki a ɓangaren ungozomanci ko karbar haihuwa da aka fi sani da ‘midwife’ , har a gangaro ƙasa zuwa kan ma’aikatan jinya wato nas-nas ɗin da muke da su.


Allah ya sani waɗannan bayin Allah suna aiki dare da rana don samar da taimakon lafiya ga al’umma. Suna yin aiki koyaushe har ma da na kwana. Ko ranakun hutu su ba sa hutawa. Amma duk wannan aiki tukurun da suke yi bai hana su fuskanci ƙalubale mai girma ba daga mutanen gari, abokan rayuwarsu (miji), dangi har ma da wuraren ayyukansu.

Babban ƙalubalen kuma shi ne kowa ba ya son ya aure ta kuma ba zai bari ko ɗansa ko ƙaninsa ko wani ɗanuwansa ya aure ta ba. Idan za a yi auren ma, ma fi yawancin lokuta sai dai a yi yarjejeniyar su ajje aikin kafin a aure su. Ko kuma idan an yi auren rashin zaman lafiya da abokin zamanta ko kishiya ko dangin miji ya sa dole idan ba a ci sa’a ba aikin zai iya salwanta. Duk da tarin amfanin da take da shi a wajen aikin.


Sanannen abu ne cewa ba inda aka fi buƙatar ma’aikatan lafiya mata sama da ƙasashen musulunci har ma da Arewacin Najeriya. Mutanen Arewacin ƙasar nan su ne suka fi kowa ƙyamar ma’aikatan lafiya maza su duba matayensu. Kuma su suka fi kowa son a ce mace ce ke duba matansu ko matan da suka dangance su.

Kuma a nan kira ya fi yawa a kan mace ta je ta yi karatun lafiya saboda duba mata masu lalura. A maimakon maza su duba su. Amma fa kowa ya ɓoye ‘ya’yansa mata, da matansa na aure da ƙannensa, yayyensa, har ma da duk wata mace da ta shafe shi. Ya hana ta ta yi karatun da ya shafi lafiya. Hakazalika kuma ba sa ƙaunar su ko ‘ya’yansu, yanuwa ko ma abokanai su auri waɗannan bayin Allah. To a ina matsalar take? Waɗannan bayin Allah suna aiki dare da rana don ceto rayukan al’umma su kuma suna cikin garari na tsangwama da ƙyama daga al’umma. Kuma ina hikimar ana son cin dankali kuma a lokaci guda ana kushe shi?

Wasu daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta sun haɗa da:

*Ƙalubale na farko shi ne a wajen aikin nata. A wurare d dama musamman ma asibitocin da ba na gwamnati ba. Wasu ba su fiye son ɗaukar mata ma aiki ba sam. Komai ƙwarewarsu sai ka ga an fi ɗaukar maza. Sai dai a ɓangarorin da ba yadda za a yi sai an ɗauki matan, Kamar nas ko ungozoma. Idan an ɗauke ta aikin ma sai a dinga tsaurara mata. idan ta nemi uzuri a kan matsalar maigidanta ko yaranta. Ko kuma idan cikinta ya tsufa ta nemi ta ɗauki hutun haihuwa. Wannan yana harzuƙa shugabannin gudanarwa na asibiti. Idan na gwamnati ne, yana ganin ta zo masa da matsalar sai ya samo madadinta. Haka idan asibiti ne mai zaman kansa yana ganin kawai asara za ta jawo masa. Dole sai ya takura wasu ma’aikatan ko kuma ya ɗauki wani ko wata da za su maye gurbinta. Kafin ta dawo daga hutun haihuwa. Amma abinda ba su gane ba shi ne, don tana aiki ƙarƙashin wani ba zai sa kuma mijinta ya ɗauke ko ya rage mata haƙƙoƙinsa da na yaransa dake kanta ba. Duk da ma’aikaciya ce, amma kuma bai hana mijinta ya nemi abinci ko kulawa da makamantansu daga gare ta ba. Haka yaranta su ma suna buƙatar kulawarta kamar sauran yaran da iyayensu ba sa aiki. Haka take rayuwarta ta hanyar raba kafa tsakanin aikinta da kula da gidanta. Amma duk da haka a kowanne ɓangare ana ganin baikenta. Maza ƙalilan ne suke ƙarfafawa matarsu ai aiki gwiwa ta hanyar fahimtarsu, kama musu dawainiyar gida da ta yara. Wasu mazan kuwa sai su bar su da ɗawainiyar kuma kullum ƙorafi.

*Matsalar dangin miji. Dangin miji kullum suna ganinta a matsayin mai yawo. Wacce ba ta zama a gidanta kamar sauran mata. Ga shi kuma ba kamar sauran ma’aikata ba, har kwana take yi. Haka za a ci gaba da tsangwamarta. Wata ma idan ta ɗauki albashinta za ta yi musu hidima amma duk da haka ba fita. Har mijinta za a dinga tunzurawa a dinga yar masa da magana. Idan ba a samu mai dakakkiyar zuciya ba sai ya huce a kanta. Ya kamata masu irin wannan su dubi Allah su daina. Su ƙarfafeta kamar yadda za su ƙarfafi ‘ya’yansu ko ‘yan uwansu na jini.

•A wajen danginta idan ba a samu masu fahimta ba, suna ganinta a matsayin wacce ba ta son shiga cikinsu saboda girman kai. Ba ta kai musu ziyara da sauransu. Ko idan ana sha’ani ba ta zuwa saboda yawan lokacin da take ]auka a wajen aiki. Kuma idan ta baro wajen aikin tana buƙatar yin wasu abubuwan a gidanta. Don haka ya kamata mutane su san wannan, kuma su dinga mata uzuri.

•A wajen mijinta ma, kamar yadda na fa]a a baya idan ba na kirki ba ne mai tausayi aka samu ba, zai ta ɗaukar aikinta a matsayin wani abu da yake shiga haƙƙinsa da na ‘ya’yansa. Idan ba a kai zuciya nesa ba za a yi ta samun saɓani. Kuma wannan ɗabi’a ba ta kamata ba. Saboda wannan mace a kullum tana fitowa filin daga domin ceto rayukan al’umma. Kasancewar zuciyarta a ɓace ko ƙwaƙwalwarta a ruɗe, zai iya sanya rayukan mutane da dama a cikin haɗari.

•A wajen marasa lafiya kuma ana zarginsu da mutane ne masu wulaƙanci. Musamman asibitin gwamnati. Wannan ba wai ina kare su ba ne. Amma a kula da cewa suna duba adadin marasa lafiyar da ya shallake hankali.

Me ya sa ba a son auren ma’aikaciyar lafiya?
Akwai wani taro da na taɓa halarta a kan yadda za a ƙarfafa wa mata gwiwa a kan su dinga karantar fannin aikin lafiya saboda su dinga taimaka wa ‘yanuwansu mata. Ana tsaka da taron sai wata daga cikin ma’aikatar lafiyar da ta daɗe ba ta auru ba ta miƙe. Ta ce da mashirya taron: “kullum kuna jan hankalinmu a kan mu yi karatun lafiya. Amma idan mun yi karatun, sai a ƙi aurenmu.” Wannan jawabin nata ya sa jikin da yawa daga mahalartan ya yi sanyi. Dalilai da dama da ya sa ba a son auren ma’aikatan lafiya. Ƙalubalen da na lissafa a baya suna ciki. Sai kuma wasu ƙari kamar haka:

  1. Tana kwana a wajen aikinta: Ba dukka mazan Hausawa ne za su yarda su auri matar da take kwana a wajen aiki ba. Saboda suna ganin rashin dacewar hakan a wajensu. Musamman ma rashin lokutan da za ta ba shi dukkan haƙƙoƙin sa na aure. Wasu ko sun yarda ‘yan zuga daga dangi da abokai sai sun zuga su a kan illar haka. Idan ba a samu mai kai zuciya nesa ba, sai ya ce ya fasa.
  2. Tana ɗaukar albashi mai tsoka. Wasu mazan da ba su da karfin zuciya kuma gani suke yi idan sun auri mace mai samun na kanta tamkar za ta fi karfin su. Kuma kamar ba za su iya juya ta ba. Wanda kuma ba haka ba ne. Shi raini da rashin biyayya ya danganta da wacece kuma yaya tarbiyyarta take.
  3. Ba ta da kamun kai: Abinda mutanenmu ba su gane ba har yanzu shi ne: Karatun boko ko aiki ba ya mai da mace mara kamun kai sai idan ita ta so. Akwai mata da yawa da suka lalace kuma ko sunansu ba su iya rubutawa ba. Ballantana a yi zancen zuzzurfan karatun boko.

In sha Allah za mu ci gaba a mako na gaba. Sannan Kuma za mu kawo muku har ma fa’idojin auren ma’aikaciya.