Walida: Abin da ya sa muka ajiye yarinyar Jigawa a waje mai tsaro – SSS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin kaya (SSS) mai suna Patrick ya bayyana dalilan da suka sanya aka ajiye wannan yarinyar ‘yar Jihar Jigawa mai suna Walida Abdullahi a hannun hukumar.

A baya ne aka yi zargin an yi garkuwa da ita tare da tilasta mata auren wani jami’in SSS, lamarin da ya haddasa cece-kuce tsakanin jama’a da ƙungiyoyi al’umma masu zaman kansu, wanda har ya kai ga samun izinin kotu na a sako ta.

Mista Patrick ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar DailyTrust bayan wani zama tsakanin SSS da wakilan ƙungiyoyin al’umma.

Ya ce, an ajiye yarinyar ne a ƙarƙashin kulawar hukumar saboda barazana ga zaman lafiyarta.

Zaman ya samu halartar wakilai daga “International Federation of Women Lawyers, FIDA, the National Youth Council of Nigeria, NYCN, the Arewa Youth Assembly”, da Walida, da kuma wasu daga cikin jami’an SSS.

Walida ta bayyana rashin gamsuwa da sake koma wa gidansu na asali saboda yadda matar mahaifinta ke musguna mata. Saidai mahaifinta ya yi watsi da ikirarin nata, inda ya ce an kitsa makirci da ita ne wajen faɗar haka.

A game da ko hukumar ta gana da iyayen Walida, mataimakin daraktan ya ce sun gana da su har sau huɗu.

A cewarsa, a majiyoyin waje ne suka jin batun zargin jami’insu da tilasta wa yarinyar auren sa, wanda ya sa tuni suka ƙaddamar da bincike akan al’amarin kuma har an gano wanda ake zargi, wato wani mai suna Ifeanyi.

By Babaji