Wane dalili ke sanya mata mantawa da Allah lokacin biki?

A halin da ake cikin yanzu, kowa, musamman samari sun tabbatar da cewa galibin mata na shiga wani yanayi na mantawa da ibada lokacin shagulgulan biki, da har ta kan kai su manta yin salla tsawon wuni guda.

An gano yadda galibin matan ke ƙin yin sallar saboda dalilan kwalliya, da yanayin hidimar bikin.

Sauran dalilan su ne yanayin kayan da matan ke sawa masu kama da tsirara, sai kuma hayaniyar wurin biki, da kuma uwa uba rashin son kada abu ya wuce su ba a yi da su ba.

Wasu na ganin cewa, kwalliya ita ce abu na farko da galibin ‘yan matan ke sanyawa su ƙauracewa yin salla. Make-up yana cinkin abun da ke hana mata yin sallah a wurin biki saboda in aka yi kwalliya ba a so a wanke ta.

Da yawa sun gwammace sallar ta wuce su da dai su wanke kwalliyar da ke fuskarsu. Make-up ne ke hana yawancin mata yin Sallah lokacin biki, wasu matan tun ƙarfe 4 suke zuwa a yi masu kwalliya duk da cewa bikin ma sai 7 ko takwas za a fara.

Suna gain wai ba zai yiwu ka ɓata irin wanna kuɗin da kuma lokacin ka ba, kuma a ce ka wanke lokaci ƙanƙani, kawai ya fi sauƙi mutum ya haɗe sallar bakiɗaya kawai. Ku ji shirme fa!

Wasu kuma na hin wai wani lokaci kai ne ke ɗaukar zafi musamman ma idan al’amuran bikin suka yi yawa. Wasu mata zirga-zirgar da suke yi don tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata ne ke sanya su mantawa da sallah. Ko da ya ke hakan ba dalili bane, amma za a ga wasu basa samun zama ne, saboda kujiba-kujiba.

Haka zalika, wasu matan sun alaƙanta ƙaucewa yin ibadar da irin kayan da matan ke sawa da ko kaɗan ba za su basu damar yin sallar ba.

Haka zalika, dalili na gaba shi ne rashin samun wurin da babu kaɗe-kaɗe a lokacin bikin, shima na ɗaya daga cikin abun da ke hana mata sallah.

Su kuma wasu matan sun ce rashin son kar a basu labarin yadda amarya ta shigo wurin biki ko yadda wani mawaƙi ya raira waƙa, kan sa su mantawa da ibada.

To, ko ma dai bisa wane dalili ne, mu sani cewa bai kamata mu bari ibada ya riƙa wuce mu kan wani abin duniya ba, saboda ita duniyar nan ba wurin zama bace. Salla a kan lokaci yana da matuƙar muhimmanci.

Wasiƙa daga BILKISU ADAM, 09070905293.