Wane ne Adolf Hitler?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afirilu na shekara 1889, ya kashe kansa ranar 30 ga watan Afirilu na shekara 1945 bayan an ci Jamus da yaki.

An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 1889 wato shekaru 122 kenan da suka gabata. An aife shi a wani gari mai suna Braunau-am Inn, a ƙasar Austriya kusa da iyakar ƙasar da Jamus. Shi ne na huɗu a gidansu. Mahaifinsa wani jami’in Custum ne, ya rasu a yayin da Hitler ke da shekaru 14 da aihuwa.

Marubuta tarihin Hilter sun ce bai yi wani dogon karatu ba, ya yi wasti da makaranta a lokacin da ya ke ɗan shekaru 16 da aihuwa.

Ya yi yarintarsa cikin matsaloli masu yawa. Ya na samun ‘yan kuɗaɗen tallafi da gwamnati ke bai wa marayu, sannan kuma ya na sana’ar zane-zane da ƙera-ƙeren hannu. Sai dai duk da cewar bai yi wani dogon karatu ba, mutum ne mai shawar karance-karance, kuma a wani lokacin har ma ya kan je ya saurari mahaurori a majalisar dokokin Austriya.

Sai dai kuma tun ya na dan samari ya ke nuna kyamar tsarin mulkin demokuraɗiyya da tsarin kominisanci.

Zuwan Hitler Jamus:

Adolf Hitler ya zo Jamus a shekara 1913, ya gudo daga Austriya domin gudun kar a ɗauke shi cikin rundunar soja da ƙasar. Ya zauna a birnin Munich na jihar Bavariya.

Ya na nan ne yaqin duniya na farko ya ɓarke a shekara 1914.

Hitler ya shiga rundunar Jamus a matsayin sojan sa kai, kuma ya nuna hazaƙa da jarumtaka kwarai a cikin harkokin soja, saboda haka ne ma ya samu lambar yabo ta musamman daga manyan sojojin ƙasar. A lokacin yaƙin duniyar, ya samu raunuka har so biyu wanda cilas aka kwantar da shi asibiti. A ƙarshen yakin ya samu galar Caporal.

Bayan ɓarkewar wani juyin juya hali a Munich, hukumomi sun kafa komiti wanda aka ɗorawa yaunin binciko gaskiyar al’amarin da ya faru. Hitler ya na daga cikin membobin wannan komiti kuma ya nuna basira kwarai ta fannin jawabin gaban jama’a.

Musamman ya shahara wajen fasa wuta kokuma yafa mata ruwa ta hanyar kalamomin baki.

Wannan baiwa ta ba shi farin jini kwarai daga mutane.

A fannin siyasa ya shiga wata aaramar jam’iyya mai suna DAP wadda ta ƙunshi ma’aikata zalla masu tsantsar aƙidar kishin ƙasa, wadda ta riki a zuwa NSDAP. Ya karɓi jagorancin wannan jam’iya a shekara 1921. Ta wannan hanya ce ya fara yada alidarsa ta Nazi.

Kasancewar sa mutum da ya shahara wajen magana, sai ya zama daya daga jigajigen ‘yan siyasa a jihar Bavariya. Sabo da ƙarfin faɗa a ji da ya fara samu, ya jaraba yin juyin mulki a birnin Munich a shekara 1923 amma ba yi nasara ba.

An cafke shi, kuma a ka zartar masa da hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku, to sai dai maimakon haka watani tara kawai ya yi ɗaure domin daga baya ya samu afuwa. Ya yi amfani da wannan dama ta zama gidan yari, inda ya rubuta wani littafi mai suna da jamusancin “Mein Kampf”, idan aka fasara da hausa, ya na nufi yaƙina, wato ma’ana a cikin wannan littafi ya bayyana dalla-dalla manufofinsa da aƙidojinsa.

A cikin manufofin Hilter ya bayana shawa ga aƙidar nan ta wani masani mai suna Darwin game da faɗi tashin rayuwa.

Hitler ya bada fifiko ga wata ƙabilar Jamus mai suna Aryenne wadda akwaita a ƙasashe da dama na yankin arewancin Turai. A tunanin Hitler duk sauran qabilu na matsayin bayi ga ƙabilar ariyawan Jamus, wadda ya ce ita ce ƙabilar da ta fi ɗaukaka a duniya, kuma itace ta kamata ta mulki duniya gabaɗaya. Hitler yayi mummunar suka ga Yahudawa wanda ya dangata da annoba a cikin rayuwa duniya saboda haka nema a lokacin yaƙin duniya na biyu ya sa aka hallaka miliyoyin Yahudawa.

A cikin wannan littafi na yaƙina Hitler ya bayyana aniyarsa ta mamaye duniya.

A wani abu mai kama da faɗuwa tayi daidai da zama, lokacin Jamus da sauran ƙasashen Turai, sun fara tsunduma cikin wata matsalar kariyar tattalin arziki. Ta la’kari da faɗakarwa da Hitler ya tsananta yi, sai jam’iyarsa ta NSDAP ta ƙara samun karvuwar daga jama’a.

Sannu a hankali magoya bayan wannan jam’iyya suka fara ɗaukar shi a matsasyin wani abin bautama.

A zaɓen da aka shirya a shekara 1930 jam’iyyar ta samu kujeru.

Wannan babban cigaba ya sa cilas shugaban ƙasar Jamus na wacen lokaci Mashal Hindenburg ya nada Hitler a matsayin shugaban gwamnatin Jamus ranar 30 ga watan Janairu na shekara 1933.

Hitler ya shimfiɗa mulkin kama karya, ya kuma haddasa ɓarkewar yaƙin duniya na biyu:

Wata ɗaya bayan da Hitler ya kama shugabancin gwamnati sai majalisar dokoki ta yi gobara.

Hitler sai ya ɗora alhakin gobara ga Marinus Van der Lubbe wani jigo a jam’yyar ‘yan communist wadda ya ke mummunar adawa da ita. Ya yi amfani da wannan dama inda ya cafke dubunan magoyan bnayan wannan jam’iyya. A washe garin wannan gobara sai shugaban ƙasar Jamus ya rattaba hannu kan dokar tabace wadda ta ba Hitler cikkaken mulki, sannan daga baya shugaban sake rattaba hannu kan wata sabuwar doka, wadda ta ba Hitler wuƙa da nama har tsawan shekaru huɗu ya gudanaa da mulki ba tare da katsalandan ɗin shugaban ƙasa ba.

Daga wannan lokaci ya fara cin karensa babu babbaka, ta hanyar shimfiɗa mulkin kama karya. Ya soke jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin ƙwadago, sannan ya yi amfani da wannan dama domin ƙara yaza manufofin jam’yyarsa.

Shugaban ƙasar Jamus Hindenburg ya rasu ranar 12 ga watan Ogusta na shekara 1934. Adolf Hitler ya yi gadonsa sannan kuma shi ke riqe da matsayin shugaban gwamnati da kuma Führer wato shugaban jam’iyyarsa.

Haƙiƙanin gaskiya Adolf Hitler shi ne ya yi sanadiyar ɓarkewar yakin duniya na biyu. Tun lokacin da ya wallafa littafinsa mai suna Yaƙina ya bayyana manufofinsa na mamayar duniya. To kuma ga shi dama ta samu, domin shine shugaban ƙasar Jamus kuma shugaban gwamnati.

A cikin burinsa na mamayar duniya, Hitler ya ƙuduri aniyar cimma wani buri da ya saka wanda aka fi sani da jamusanci da suna Anschluss: wato ya haɗe Jamus da ƙasashen masu makwabtaka da ita kamarsu Austriya da Chekoslobakiya.

Banda wannan ƙasashe ya aika dakarun Jamus domin mamaye ƙasashe kamarsu Poland, Danmark, Beljima, da Faransa.

Mamayar ƙasar Poland daga nan ne yaƙin duniya na biyu ya ɓarke, bayan da. A dalili da hakan ne yaƙin duniya na biyu ya ɓarke a shekara 1939.

An yi ta gwabza faɗa tsakanin dakarun Jamus da sauran sojojin kawance har zuwa shekara 1945, inda Jamus ta yi saranda.

Marubuta tarihin Hitler sun ce ya kashe kansa a cikin gidansa na ƙarƙashin ƙasa ranar 30 ga watan Afrilu na shekara 1945, amma akwai mahaura game da mutuwar tasa.

Wata ruwaya ta ce ba a wannan rana ne Hitler ya mutu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *