Da yawan mawaƙan Arewa ba su san ta yadda za su amfana da basirarsu ba – Haidar Blog

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano

Fasihin mawaqin Hausa, kuma ɗan kasuwar dake dillancin waƙoƙin Hausa a yanar gizo, mai suna Aliyu Abubakar, da ake wa laƙabi da Haidar Blog, ya bayyana wannan kyakkyawan fata da buri da yake da shi ne a kan mawaqa da dukkan waɗanda Allah Ya yi wa baiwar basirar na suna amfanuwa da basirar tasu don ƙara samun ƙwarin gwiwa gare su. Tare kuma da yin kira ga matasa da su ƙara ƙaimi wajen neman ilimi, wanda da shi ne rayuwar bawa take yin haske kuma komai ke zuwar masa a sauqaqe, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.

MANHAJA: Wane ne Haidar Blogger, cikakken suna da taƙaitaccen tarihinka?

HAIDAR BLOG: To a taƙaice dai asalin sunana shi ne, Aliyu Haidar Abubakar. Kuma asalina haifaffen Garin Zaria ne, a wata unguwa mai duna Gyellesu. Na yi makarantar primary har zuwa secondary. Sannan yanzu haka ina ci gaba da karatu na a ABU Zaria. Sunana na Haidar Blog ya samo asali ne tun lokacin da muke secondary saboda ina son Ilimi a kan na’ura mai ƙwaƙwalwa, wato ‘computer’. Don haka sai na kasance mai bincike da bin ƙwaƙƙafi a kan ‘computer’ tun wancan lolacin. Hakan ya taimaka min sosai wajen sanin abubuwa da dama da suka shafi ‘computer’, har ma na yi wani website mai suna HaidarBlog a inda nake rubuce-rubucena a kan harkar Entertainment. Toh ka ji yadda na samo sunan Haidarblog.

Sunan Haidar Blog sananne ne cikin mawaƙa da ma industry. To ya aka yi ka tsinci kanka a cikinsu?

To, farkon fara waqena dai na fara ne da yin waƙoƙin yabon fiyayyan halitta (S.A.W.) tun a makarantar Islamiyya. Daga nan kuma son waƙa ya shiga raina ya zauna daram, har ya kai ni ga shiga cikin mawaƙa ina ƙulla abota da su. Don dama ka san ‘yan Hausa suka ce “Ba a abota sai hali ko ra’ayi sun zo ɗaya.”

To wacce waƙa ka fara rubutawa, kuma cikin tarin waƙoƙin naka wacce ce bakandamiyarka?

To waƙar da na fara rubutawa da hannuna ita ce ‘Sayyid Anami’ wacce take ta yabo ce tsantsa ga fiyayyan halitta. Allah Ya sa ya cece mu a ranar da babu wani maceci bayan shi, amin. Amma waƙar da na fara shiga ‘studio’ na rera ta, ba ni na rubuta ta ba, abokina ‘Ghali Ladabin Bege’ shi ne ya rubuta ta ni kuma na rera. Bakandamiya a cikin tarin waƙoƙina kuwa ita ce wacce na yi mata laƙabi da ‘Diwani’.

To ya batum waƙoƙin nanaye, ko na ce waƙoƙin soyayya?

Nakan rubuta waƙoƙin soyayya, amma dai ba ni nake rerawa ba.

Da alama ka fi karkata ga waƙoƙin yabo. To ya aka yi ka yi kicin-kicin a cikin harkokin waƙoƙin da ba na yabo ba?

Eh Toh, ni mutum ne mai son ganin masu basira suna amfanuwa da basirarsu. To don haka sai na kutsa ciki. Bincike, na yi binkice na ga da yawan mawakan Arewa ba su san ta ya ya kamata a ce sun amfana da basirarsu ba. To a nan ne na fara binkicen waɗanne hanyoyi ne ake samun kuɗi da waƙa? Ma’ana yaya za a yi mawaƙi ya sayar da waƙar sa a Internet, tunda yanzu babu CD, babu cassette. A haka kuma Allah da ikon sa muka yi binkice. Har dai ma na yi makaranta a ‘Online’, a kan yadda zan bi wajen siyar da waƙa a ‘online’ da dai sauransu.

To yanzu ya kasuwancin waƙoƙin yake a yanar gizo, shin ko kwalliya na biyan kuɗin sabulu?

Eh a gaskiya tana biya, amma ga Wanda ya san yadda zai bi ya samu kuɗi. Sakamakon da yawan mawakan mu na arewa wasu ba su san yadda na za su Distribution ɗin waƙa ba. Ballan tana a ce promotions (marketing), ko Music Publishing, ko syc licensing.

To a matsayinku na manyan mawaƙan dake da ido a kan yadda za a tafi da zamani, ko akwai wani taimako da kuke ba wa matasan mawaƙa musamman ta ɓangaren ‘marketing’ a yanar gizo?

Eh sosai ma kuwa. Muna iya yin mu wajen nuna wa da yawansu hanyoyi da ya kamata su bi wajen tallata kansu da hajojinsu ba tare da sun biya ko sisi ta hanyar yanar gizo. Wasu kuma sukan biya mu mu yi musu ‘Promotion’ ko kuma mu zama manager ɗinsu. Ban da haka ma, nakan bayar da ‘courses’ a ‘online’, kamar a zoom meeting da wasu mawaka Ko kuma ‘Artist Management’. Don yanzu haka Ina Management na Artist kamar Kawu Ɗan Sarki, Sani Ahmad, Zainab Ambato, Rabil Jo’s, da dai sauransu. Ma’ana ni ne mai kula da ‘music distribution’, music publishing’, ‘Music copyright’, ‘Sync licensing’ da ‘social media management’ nasu.