Daga CMG HAUSA
Yau ne, mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na hukumar tattalin arziki da zaman takewar al’umma ta yankin Asiya da tekun Pacifik ta MƊD wato ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo a birnin Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong dake kudancin ƙasar Sin, inda ya gabatar da jawabi.
Cikin jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, ya dace a hada kai domin gina kyakkyawar makomar ƙasashen yankin Asiya da tekun Pacifik, ta hanyar ɗaukar matakai uku, na farko, nacewa kan manufar kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare kuma da nuna adawa ga yunƙurin tayar da hankali a tsakanin rukunonin aikin soja cikin yankin na Asiya da tekun Pacifik, na biyu, sanya ƙoƙari tare domin ingiza ci gaban tattalin arziki, da gina yankin ciniki maras shinge a yankin, na uku, ƙasashen da abin ya shafa dake yankin, su hada kai domin gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za su cimma burin samun moriya tare.
Kana Wang Yi ya jaddada cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace, domin ba da ƙarin gudummowa kan tabbatar da dauwamammen ci gaba da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
