Wasan ƙanin miji (1)

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkan mu da sake haɗuwa a shafin iyali na jaridar al’umma. Allah ya kawo zaman lafiya a rayuwar gidan aurenmu, ya kuma albarkaci ‘ya’yanmu.

A yau dai za mu taɓo wata al’ada ta malam Bahaushe, al’adar da ta samo asali da ‘isnadin’ sa mai tsayi ne a lardin Hausa.

Ba ko wacce ba ce face wasar ƙanin miji. A yadda na ke ji a wurin tsofafi, al’ada ce da ta samu wurin zama a Ƙasar Hausa, har ta kai suke ganin aibata ta tamkar wani saɓo.

Ita wannan al’ada ta wasa tsakanin matar yaya da ƙanin miji, wata ɗabi’a ce da ta fi kama da auratayyar wasan kwaikwayo, inda ƙanin miji zai hau kujerar yayansa cikin barkwanci.

A shekarun baya, a wasu garuruwa na Hausawa, ƙanin miji ne ke hawa kujerar mulkin maigida idan ba ya kusa, hakan ta sa bayan kwanon maigida, ba kwanon da ya kai na ƙanin miji daraja. Albarkacin wannan al’ada ƙanin miji ke da damar shigo wa da abokai a gidan yayanshi, su yi yadda suke so. Hakazalika wannan al’ada ce ta ba wa ƙanin maigida damar wasa da matar yayarsa, ko da kuwa ta girme shi. Ƙaramin maigida kenan.

Menene dalilin samuwar wannan al’ada?
Zumunci wani sanannen hali ne na malam Bahaushe, wannan ne ya sa yake darajanta alaƙa ko da ta kasuwanci ce. Muhimmancin sanayya da Bahaushe ya sani ya sa yake mayar da ɗan wani na sa. Don haka a ƙoƙarin ƙarfafa ‘yan’uwantaka tsakanin wa da ƙani ya sa ya ƙirƙri wannan al’ada. A na sa gani, ta hakan ne zai sa zumuncin ‘yan’uwa ya ɗore har ɗiya da jikoki. Wannan ne ya sa ba za a iya kushe niyar ta sa ba, domin alkhairi ne ƙudurinsa.

Sai dai a nan Bahaushe ya yi tuya, ya manta da albasa, saboda ya manta da illar kusancin mace da namijin da ya kasance ‘ajnnabi’ gare ta. Wannan kusanci kan ba wa shaiɗan damar kunna wutar sha’awa a tsakaninsu, kuma lokuta da dama yana samun galaba. Domin kusan ince kaso mai yawa na zinar-aure da ke wakana a gidajen Hausawa ta tsakanin ‘yan’uwa ce. dalili, an bi son rai a zamantakewar.

Maigida ya killace matarsa, ba ta fita barkatai, ya toshe hanyoyin da za ta iya fita ta yi ɓarna, amma ya bar baligin ƙaninsa na shiga gidan ba tare da izini ba, ba ruwansa da halin da matar ta ke ciki a lokacin da ƙanin na sa zai shigo.

Shin ta suturta jikinta, ko ta rufe kanta, yaushe ya kamata ya shigo, kuma yaushe ya kamata ya bar gidan, a ganinsa ƙaninsa ne, don haka a cikin ko wane irin yanayi zai iya ganin matarsa, kuma zai iya kiran kansa mijinta. Saboda dai ƙanin mijinta ne.

Abin tambaya a nan, shin ƙanin miji ba namji ba ne mai sha’awa, ko kuwa matarka ƙanwarsa ce ta jini? Wasar da suke yi kawai ta isa dasa sha’awa a zuciya mai rauni, bare kuma yana shigowa gidan ya ganta a ko wane irin shiga, wasu lokuta ma da ɗaura-gaba, to ta ya za a iya kawar da yiwar ɗigar sha’awa a zuciyarsu.