Dokar Zaɓe: Kada ku ɗauki matsayar Buhari da rashin muhimmaci, gargaɗin Jega ga ‘yan Majalisun Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Attahiru Jega, ya faɗa wa Majalisar Tarayya cewa ɗaukar matsayar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari game da batun yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima da rashin muhimmanci ba ita ce hanya mai ɓulewa ba ga ƙasar nan.

Jega ya yi wannan furici ne a wajen wani taro kan Dokar Zaɓe ta 2021 wanda cibiyar Yiaga Africa tare da abokan hulɗarta suka shirya ranar Lahadi a Abuja.

A cewar Jega, lamarin zai fi yi wa ƙasa armashi idan ta shiga sha’anin zaɓe na gaba da sabuwar dokar zaɓe, yana mai cew hakan zai ɗaga daraja da kuma inganta shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓukan.

Ya ci gaba da cewa, dokar na ƙunshe da abubuwa masu matuƙar muhimmanci waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin zaɓe baya ga salon zaɓen fidda gwani na ‘yar tinke, don kuwa Nijeriya ba ta samu wani ingantaccen cigaba ba game da dokar zaɓe tun 2010.

“Zai fiye wa Nijeriya alheri idan muka yi amfani da tsarin ‘yar tinke yadda ya kamata wajen zaɓen fidda gwani, ‘yan Majalisar Tarayya na da masaniyar cewa gwmanoni kan murɗe zaɓen fidda gwani da akan yi cikin sirri wanda hakan ya sa suke tunani idan aka koma yin zaɓen bisa tsarin ‘yar tinke hakan zai kuɓutar da su daga murɗiyar da akan yi a wancan tsarin.

“Amma kuma akwai buƙatar mu tsananta nazari da kyau a kan wannan yanayi, don haks’a shawarata a nan ita ce a miƙa wa INEC wannan doka don ta soma shirye-shiryen zaɓuɓɓukan 2023.”

Ya ci gaba da cewa, “Hanya mafi sauƙi da za a aiwatar da wannan kuwa shi ne kada a danne ra’ayin shugaban ƙasa, amma dai a ajiye batun tsarin zaɓen fidda gwani na ‘yar tinke a gefe har zuwa lokacin da muka tabbatar da cewa lallai jam’iyyu za su iya aiwatar da hakan.

“Ba zai yiwu ka haɗa jariri da ruwan wanka ka zubar ba, kada mu bari batun tsarin zaɓen ‘yar tinke ya sa mu rasa muhimman abubuwa da dokar ta ƙunsa.

“Akwai buƙatar hakan ne domin samun dokar da za a miƙa wa INEC don soma shirye-shiryen zaɓuɓɓukan 2023.”

Do’a wannan Jega ya yi kira ga Majalisar Tarayyar da ta duba sannan ta yi abin da ya dace maimakon damuwa da batun wani sashen dokar da Shugaban Ƙasa ya ƙi yarda da shi.