2023: Umahi ya yi wa Tinubu gugar zana

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ya kamata ‘yan siyasar Nijeriya su tsayar da shekarun yin murabus daga harkokin siyasa maimakon su ci gaba da fafutukar neman tara kuɗi har na tsawon rayuwarsu.

Gwamna Umahi ya yi waɗannan kalaman ne yayin wani shiri da gidan talabijin ɗin Channels ya yi da shi a ranar Litinin wanda ake ganin gugar zana ce ya yi ga dattijon ƙasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Cif Bola Tinubu, wanda ya nuna kwaɗayinsa kan mulkin ƙasa lamarin da, da daman ‘yan ƙasa ke ra’ayin cewa ai ya tsufa game da sha’anin riƙe mulkin ƙasa.

Don haka ya yi kira ga masu riƙe da muƙaman siyasa a Nijeriya da su duba su soma ɗora yaransu a kan hanya don ba su damar sanin mece ce ainihin rayuwa.

A cewar Umahi, “Abin dariya ne a wannan ƙasa ganin yadda wasu mutane shekarunsu sun ja amma duk da haka ba su daddara ba wajen fafutukar neman kuɗi. Cewa nake idan mutum ya tsufa kamata ya yi mu riƙa ƙoƙarin ganin yadda za mu daidaita tsakaninmu da Ubangiji da kuma gode maSa dangane da damar da Ya ba mu.

“Ya kamata mu soma duban lamarin ta fuskar cewa, idan ka samu nasarar rayuwa ya zamana ‘ya’yanka ba su samu nasarar ba, tamkar kai ma ba kai nasara ba ne. Dole mu bari jama’a su san rayuwa haƙiƙaninta, babu wanda zai tafi kabarinsa da kuɗi aikinka ne zai bayyana ko kai wane ne sannan ya yi tasiri ga ‘ya’yanka da kuma zamanin da ka rayu a cikinsa.

“Wannan shi ne irin abin da ya kamata mu yi don jama’a su fahimci cewa ita rayuwa ba ta taƙaita a kan kuɗi kawai ba, tare da sanin cewa Allah ne ke ba mu duk wani muƙami kuma zai tambaye mu a kan yadda muka riƙe muƙaman.”

Ya ƙara da cewa, “A wannan ƙasa ba a ƙayyade shekarun da za mu ce mun yi ritaya ba, haka muke ci gaba da faman neman kuɗi har iya tsawon rayuwarmu.

“Ba wai na taƙaita a kan shugabancin siyasa ba ne kawai, a rayuwa kamata ya yi idan ka cimma wasu shekaru, ka ji cewa ya kamata ka huta don bai wa ‘yan baya dama.”

Ko da aka tambayi Umahi ko ya san wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kamata ya yi ritaya don bai wa ‘yan baya damar a dama da su, sai ya ce, “Wannan ba ya zuciyata kwata-kwata.”