Yaƙi da cutar Kwalara

A Nijeriya, an sake samun ɓullar cutar Kwalara da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu sama da dubu a faɗin jihohin ƙasar.

Alƙaluman baya-bayan nan da Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya NCDC ta fitar, sun bada wani rahoto mai muni na kamuwar mutum 1,141 da cutar, sannan 30 sun mutu a ƙananan hukumomi 96 a cikin jihohi 30.

Wannan lamari da ya shafi lafiyar jama’a gabaɗaya, akwai gazawar tsarin samar da tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli.

Jihohin da suka fi fama da wannan annoba – Bayelsa, Zamfara, Abia, Kuros Ribas, Bauchi, Delta, Katsina, Imo, Nasarawa da Legas – su ne ke da kashi 90 cikin 100 na cutar kwalara.

Amma wannan annoba bai tsaya a waɗannan jihohi 10 kaɗai ba, babu wani lungu da saƙo na ƙasar da wannan cuta ba ta leƙa ba, yayin da ake rasa ruwa mai tsafta da tsaftar muhalli.

Ba sai an ce ba, a ra’ayinmu, dole ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don guje wa sake afkuwar lamarin da ya faru a shekarar 2010. Mun tuna cewa a waccan shekarar, Nijeriya ta sami ɓullar cutar kwalara mafi muni inda kusan mutane 40,000 suka kamu da cutar sannan sama da 1,500 suka mutu, a cewar wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya.

A shekarar 2014, Nijeriya ta samu mutane 35,996 da suka kamu da cutar sannan a shekarar 2015 an samu cullar cutar guda 2,108, yayin da 97 suka mutu. Ba sai an faɗi, cutar kwalara ta zama ɗaya daga cikin manyan cututuka da suke kawo ƙalubalen kiwon lafiya na ƙasar.

Yana da kyau a lura cewa cutar kwalara, cuta ce da ke ƙarar da ruwan jikin ɗan adam, wanda ake sami ta hanyar shan ƙwayoyin cuta na ‘Ɓibrio cholerae’. Ana samunsa ne a wuraren da ba su da tsafta da gurɓatattun hanyoyin ruwa.

Yayin da ruwan sama ya tsananta, haɗarin cigaba da yaɗuwa cutar yana ƙaruwa, wanda ke nuna ya kamata a yi gaggawar ɗaukar matakan da suka dace.

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH) ta samu matsalolin cutar, inda ta ayyana dokar ta-ɓaci da kuma shirye-shiryen yaƙi da cutar kwalara a jihar.

Matakan sa ido na LASUTH abin yabawa ne, amma bai kamata su zama dole ba a cikin al’ummar da ke da albarkatu da iya aiki kamar yadda ya bayyana a Nijeriya.

Gwamnatin jihar Legas ta kuma yi kira da a ƙara sanya ido da kuma ɗaukar matakan kariya don daƙile ɓarkewar annobar a ƙananan hukumomin Eti Osa, Legas Island, Ikorodu, da Kosofe.

A namu ra’ayin, wannan annoba bala’i ce ga lafiyar jama’a, da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin kiyaye rayuwar jama’a.

Ta yaya al’ummar da ke da arzikin albarkatun ƙasa kamar Nijeriya za ta cigaba da fama da cutar da aka kawar da ita a sassan duniya shakaru aru-aru? Mun yi wannan tambayar ne bisa la’akari da irin yadda gwamnati ke zuba ido a kan lamarin, wanda ke nuna kamar ana siyasantar da al’amuran da suka shafi rayuwar talakawan ƙasa bakiɗaya.

Ruwa mai tsafta, babban haƙƙin ɗan adam, ya kasance abin jin daɗi ga ‘yan Nijeriya da yawa. Gurɓatattun tsarin samar da ruwa, da rashin isassun wuraren jinya suna cigaba da dawwamar muggan cututtuka na ruwa kamar kwalara.

Muna ba da shawara mai ƙarfi cewa ya kamata a yi ƙoƙari na haɗin gwiwa daga duk masu ruwa da tsaki – gwamnati, masu bada kiwon lafiya, ƙungiyoyin jama’a, da sauran su.

Su ma ‘yan Nijeriya, suna da rawar da za su taka wajen daƙile wannan annoba. Bin tsarin tsaftar da ya dace, bayar da shawarwari don inganta tsaftar muhalli a cikin al’ummominsu, da kuma ɗorawa hukumomi alhakin magance waɗannan matsaloli. Matakai ne masu matuƙar muhimmanci ga Nijeriya don kawar da ɓutar kwalara bakiɗaya.

Leave a Reply