Yadda aka fara haska fim ɗin Fanan a Sinima

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

A yanzu haka dai an fara haska shahararren fim ɗin  ‘FANAN’ a Cinimar Platinium da ke kan titin Zaria, kusa da Masallacin Umar Bin Khaddab da ke cikin garin Kano.

An daɗe dai ana ta sanar da bayyanar fim ɗin wanda aka shirya shi tare da kammala aikin sa kusan shekaru biyu da suka gabata. Kuma an ƙiyasta fim ɗin ya laƙume miliyoyin Naira.

Fim ɗin dai na tsohuwar jaruma Mansurah Isah ne, wanda aka shirya shi a ƙarkashin kamfanin ‘Today’s Life’ tare da haɗin gwiwar wasu kamfanoni domin samun ingantuwar aikin.

A lokacin da muka ji ta bakin babbar Furodusan fim ɗin Mansurah Isah, a kan manufar ta ta shirya wannan fim ɗin ta bayyana mana cewar, “Manufar shirya wannan fim ɗin dai na ‘Fanan’ shi ne, kawo gyara a cikin Matsalolin rayuwar mu na yau da kullum.

Domin ni shirya fim a wajena ba sabon abu ba ne, don na daɗe ina shirya fim don faɗakar da jama’a. Don ba zan manta ba fim ɗin da na yi na baya bayan nan shi ne ‘Akila’ wanda ya tavo zamantakewar auren da kuma ƙalubalen da yara su ke samu idan aka kasa samun jituwa a tsakanin miji da mata.

“To a gaskiya wannan fim ɗin na ‘Akila’ ya shiga zuciyar mutane sosai, domin kuwa mata da yawa sun kira ni a waya suna yi mini godiya, saboda akwai wadda ta faɗa mini cewar, da suka kalli fim ɗin ita da mijin ta sai suka samu zaman lafiya, saboda irin matsalar da su ke fuskanta kenan, amma daga lokacin da suka kalli fim ɗin sai suka tsara yadda za su shawo kan matsalar su.”

Ta ci gaba da cewa, “To wannan ce ta ba ni damar shirya wannan fim ɗin na ‘Fanan’ wanda ya ƙunshi matsalolin rayuwar cikin gida kuma yana da saqo mai gamsarwa. Daman babban buri na dai a rinƙa samar da fina-finai masu inganci da ma’ana, don haka ne ma idan ka kula wannan fim ɗin ya ci kuɗi sosai wajen aikin sa, don kawai mu samu aiki mai ingancin da zai isar da saƙo mai ma’anar da zai gamsar da masu kallo, kuma idan har aka ci gaba da yin fina-finai masu inganci, to hakan zai sa ita kanta masana’antar ta sauya daga inda take a yanzu.”

Dangane da jaruman fim ɗin kuwa, Mansurah Isah ta ce “Mun yi amfani da ƙwararrun jarumai kamar Sani Danja, Yakubu Muhammad, Ali Nuhu, Sabira, Khadijatul Iman Sani Danja, Khalifa Sani Danja, Rahama M K, Saratu Gidado, Tijjani Faraga, da sauran fitattun jarumai.”

Ko ya Mansurah ta ke kallon karɓuwar fim ɗin ‘Fanan’ a wajen Jama’a? “To gaskiya alhamdu lillah, babu abin da zan ce sai qarfin gwiwa da na ke da shi na karvuwar fim ɗin, domin tun lokacin da waƙar ta fito aka sake ta, mutane su ke ta rububin ta wannan ya nuna alamar nasara ga karɓuwar fim ɗin.

“Don abin da ya fi ba ni mamaki ma, a lokacin da na saka waƙar a shafina, sai kawai na ji kira daga Villa wato fadar Shugaban ƙasa, aka sanar da ni cewar Aisha Buhari ta ce na kawo waqar fim ɗina da ta ga na ɗora, kuma daman muna magana da ita idan aikin Gidauniyar ta ya tashi. To na za ta wannan aikin ne ya tashi, amma da na tura kafin wani lokaci sai aka riƙa kira na ana faɗa mini cewar Matar Shugaban Ƙasa ta saka waƙar ‘Fanan’ a shafinta.

“Wannan abin ya ba ni mamaki, domin ta wannan sakawa da ta yi waƙar fim ɗin ta samu karɓuwa sosai a duniya, don haka na ke ganin fitowar fim ɗin zai zamo da nasara.”

Mun tambaye ta ganin an kashe kuɗi a wajen aikin fim ɗin kuma ga shi kasuwar fim ta mutu sai da Cinima da sauran ɗan abin da ba za a rasa ba. Ko ta ina za ta mayar da kuɗin da ta kashe? “To gaskiya kasuwar fim ta mutu, sai dai akwai hanyoyi na dabaru da mu ke bi don ganin ko da ba a ci riba ba to aƙalla ya zamo an mayar da kuɗin da aka kashe, don haka, bayan Cinima za mu saka shi a ‘YouTube’, kuma mu sayar da shi a gidajen talbijin da mu ke da su a yanzu, wanda su ma wata dama ce ta samun dawowar kuɗin fim a yanzu, amma dai muna fatan za mu cimma nasara, kamar yadda a yanzu muka fara da Cinima, haka za mu ci gaba da bin hanyoyin da za mu yaɗa shi ga Jama’a don ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.”

Daga ƙarshe Mansurah ta yi godiya ga dukkan jama’ar da suka bayar da gudunmawarsu wajen aikin fim ɗin tun daga farkonsa har zuwa ƙarshensa.