Yadda zaɓen ƙungiyar MOPPAN reshen Abuja ya gudana

Daga IBRAHIM HAMISU a Abuja

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya Fina-finai ta Nijeriya, Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) reshen Abuja ta gudanar da zaɓen shugabanni a ranar Asabar 30 ga Oktoba, 2021, a harabar ɗakin taro na kamfanin Kufaina Films da ke Abuja.

Malaman zaɓen dai sun fara tantance ‘yan takara da misalin ƙarfe 10:30 na safe. An kuma kammala tantance su ne zuwa ƙarfe 11:30, inda aka tantance ‘yan takara guda 10.

An fara kaɗa ƙuri’a ne da misalin 11:30 na safiyar a ƙarƙashin kulawar Babban Ma’ajin ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa, Alhaji Bala Mu’azu Kufaina.

Bayan ƙirga ƙuri’un ne dai aka bayyana shugaban majalisar dokoki na cikin fim ɗin ‘Kwana 90’, wato Hon. Sharif Auwal Falala, a matsayin sabon Shugaba, yayin da zaɓaɓɓun shugabannin suka haɗa da:
Shugaba – Sharif Auwal Falala
Mataimakin shugaba – Nasir S.Gwangwazo (Editan Jaridar Manhaja)
Magatakarda – Munnir Isah
Mataimakin Magatakarda – Muhammad Sabo
Ma’aji – Balaraba Abdullahi
Sakataren Kuɗi – Abubakar Waziri Bado 
Jami’in yaɗa labarai – Abubakar A. Zazzau
Jami’ar Walwala – Zainab Mohammad
Mai Binciken Kuɗi I – Ahmad Tijjani Imam
Mai Binciken Kuɗi II – Anas B.Yusuf
Dukkanin ‘yan takarar sun nuna gamsuwa da yadda zaɓen ya gudana da kuma yadda a ka bayyana sakamakon.

Alhaji Bala Mu’azu shi ne shugaban zaɓen kuma Ma’ajin MOPPAN na Ƙasa, sannan kuma wanda ya wakilci shugaba mai barin gado, wato Alhaji Habibu Barde Muhammad Azare, wanda bai nemi tsaya wa takarar ba, saboda yana takarar Mataimakin Shugaba na Ƙasa Mai Kula da Shiyyar Arewa Ta Tsakiya.

A jawabin da Alhaji Bala ya gabatar bayan kammala sanar da zaɓen, ya yaba da yadda zaɓen ya gudana tare da yi wa sababbin zaɓaɓɓun shugabannin fatan alheri a tsawon lokacin da za su gudanar da aikinsu.

Haka zalika, ya tabbatar musu da cewa, ƙofa a buɗe ta ke ta neman shawarwari a koda yaushe daga mataki na ƙasa.

Sharif Auwal Falala

Shi ma a nasa jawabin, sabon zaɓaɓɓen shugaban MOPPAN shiyyar Abuja, Alhaji Sharif Auwal Falala, ya sha alwashin yin aiki tuƙuru gami da jajircewa, don ganin ƙungiyar ta samu cigaban da ba a tsammani. 

Ya kuma yi alqawarin bin dokokin ƙungiya da shugabanci na ƙasa da na jiha, sannan ya roƙi shugabannin da ka zaɓe shi tare da su da ma na ƙasa da su taimaka musu da shawarwari da ƙarfafa gwiwa, don ganin sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. 

Sannan ya yi alƙawarin kai ziyara ga magabata a cikin sana’ar, don karɓar shawarwarinsu.

Shi ma da ya ke tofa albarkacin bakinsa, fitaccen jarumin nan na Kannywood kuma ɗaya daga cikin waɗanda a ka zaɓa a muƙamin Sakataren Kuɗi, wato Abubakar Waziri Bado, wanda jama’a suka fi sanin sa da Allah-ya-hana-babu, ya yi kira ga abokan tafiyar, wato waɗanda a ka zaɓe su tare da su ƙarfafa wannan tafiya ta MOPPAN kuma su ji a ransu za su iya kawo ci gaba da canji a wannan masana’anta mai ɗorewa.

Taron dai ya samu halartar membobin wannan ƙungiya maza da mata da kuma masu ruwa da tsaki a wannan yanki na Babban Birnin Tarayya Abuja. An tashi taro lafiya!