Yadda aka gudanar da bikin Ƙaramar Sallah a fadar Tsibirin Gobir

Daga MUKHTAR YAKUBU

Bukukawan sallah wani abu ne da yake da muhimmanci a fadar sarautar Hausa wanda aka shafe tsawon shekaru ana yi domin raya al’adun Hausawa da muka gada iyaye da kakanni.

Dukkan masarautun da suke ƙasar Hausa da ma wadanda suke kewaye da su suna gudanar da irin nasu bikin, sai dai na wata masarautar ya sha bambam da yadda wata take gudanar da nata bikin. Wannan ya sa manyan mutane da masu yawon buɗe idanu daga ƙasashen duniya suke halartar bukukawan sallah a ƙasar Hausa. 

Masarautar Gobir dake Tsibirin Gobir a Jihar Maraɗi dake Jamhuriyar Nijar tana cikin masarauta mafi tsawon tarihi da daɗewa a ƙasar Hausa, saboda tsawon shekarun da masarautar take da shi wanda a bisa bincike na masu tarihi babu wata masarautar da ta kai ta daɗewa a yanzu.

Taron biki

Kamar yadda a kowacce shekara a bana ma Sarkin Tsibirin Gobir Sultan Abdou Bala Marafa ya gudanar bikin ƙaramar sallah a fadar sa wanda kuma ya zama mafi cikar da aka daɗe ba a yi kamar sa ba. Amma dai daman shagalin bikin sallah Tsibirin Gobir yana da ɗan bambanci da sauran na masarautu don a baya bikin sallah ana ɗaukar tsawon kwanaki goma ana gudanar da shi ne, ko da yake a can baya ma tarihi ya nuna ana yin wata guda ne wajen gudanar da bikin amma dai a yanzu yanzu ya tafi da abubuwa da dama, don haka a yanzu ana yin sati guda ne ko ƙasa da haka wajen gudanar da bikin sallar.

A wannan shekarar dai an fara bikin ƙaramar sallah ne a ranar Asabar bayan da aka bayar da sanarwar ganin wata a hukumance a ƙasar ta Nijar, wanda a tsarin masarautar idan har aka tabbatar da sanarwar ganin wata ranar Jajibere kenan. Sarki ya kan yi hawa na musamman ya kai ziyara gidan Sarkin Maƙera a cikin daren ganin wata kenan. Domin a tsarin masarautar Tsibirin Gobir Sarkin Maƙera yana da darajar da a ke yin hawa na musamman ranar jajibere a je a gaishe shi, to haka aka yi a wannan sallah in da aka kai tambura sarki ya kai ziyarar gaisuwa gidan Maƙera aka buga tambura shaidar cewa an ga wata, kuma hakan ya tabbatar gobe za a yi hawan sallah.

Sultan na Tsibirin Gobir, Alh Abdou marafa tare da Aminu Ala

An yi tafiyar cikin dare kuma cikin wani tsari na kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da raye-raye na gargajiya cikin shiga ta isa da ƙasaita, ana tafiya ana tsayawa, wani lokacin ma ana cikin tafiyar, sai a dawo baya da haka har a je gidan Sarkin Maƙera, kuma mai Martaba Sultan Abdou Marafa ya buga tambura sau biyu wadda take nuna alamar sanarwar ganin wata, kuma daga nan sai sarki ya dawo gida domin shirin hawan idin da za a yi da safe.

A ranar Lahadi da safe Sultan Abdou Marafa ya yi fitowar zuwa masallacin Idi wadda bisa al’ada Sultan yana fitowa ne da alkyabba da hula a aan sa a kan farin doki yana tafiya masallaci kan sa a rufe da hular alkyabbar sa ana tafiya ana zikiri har zuwa masallaci, kuma Sarkin Gobir ana yi masa tanti wanda a ciki yake zama shi da mutanen sa, don gudanar da sallar, kuma bayan an gama sallah akwa ɗamara da sarki yake yi ta shirin yaqi domin sarki yana dawowa ne cikin shirin yaƙi saboda haka bayan an idar da sallah sarki yana sauya kaya ne ba kayan da ya je da shi masallaci ba, don haka a cikin wannan tantin sarki yake sauya kaya, don wasu ɗamarun da a ke yi na yaqi ba za a saka su ba a yi sallah da su, don haka a ke sauya kaya a yi rawani mai fari da baqi a saka janjami, sai kuma a kawo masa doki baƙi ya hau, sai kuma a yi da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, da haka za a koma gida. 

Kuma a hanyar sa ta komawa gida yakan bi wasu hanyoyin da yake zagaya gari saboda nuna farin cikin sallah. Shi kuma sarkin masu kiɗa mai suna Gobiru yana jan tawagar makaɗa, duk da tafiyar ba mai tsayi ba ce amma saboda ana yin gaba ana dawowa baya, ana shafe tsawon wuci guda cikin wannan tafiyar.

Aminu Ala a tsakiyar mahalarta

Bayan sarki ya koma gida yana sauka a ƙofar gida yana yi wa mutane jawabin barka da sallah tare da yin nasiha da kuma godiya daga ƙarshe a yi addu’ar shekara da kuma fatan alheri, sai kuma sarki ya shiga gida ya ɗan huta.

Duk da haka dai hawan bai ƙare ba, domin bayan hutawar sarki zai fito ya karɓi gaisuwa daga hakiman sa da sauran jama’a, sai kuma a ci gaba da biki na ɗan wani lokaci sai kuma a sallami jama’a, daga nan an kammala hawan ranar sallah.

A ranar ɗaya ga sallah a ke gudanar da bikin al’adu, wanda a ranar, Runjawa suna zuwa su yi hawan qaho da masu kaɗe-kaɗe da raye raye irin su ‘yan tauri za su zo su yi, da masu kiɗan kurya da Maƙera su zo su yi wasa wuta da abubuwa na ban al’ ajabi sauran su, kowa zai zo ya nuna bajintar sa.

Sarkin Tsibirin Gobir a tsakanin al’ummarsa yayin taro

Daga nan sai kuma Inna shugabar ‘yan bori, koda yake ita sarauta ce ta shugabar mata a masarautar, amma an fi rinjayar da ita ga ‘yan bori amma dai ita ba bori take yi ba, amma da yake su mata ‘yan bori idan sun zo suna ƙarƙashin kulawar ta da sauran matsafa, sai aka bar mata kula da su, don a Tsibirin Gobir ana da sarautar mata wajen guda takwas  akwai irin su mai tsamiya da tazabga da ita Inna, akwai Magajiya, akwai Magajiyar Girma da Magajiya ƙarama da makamantan su.

To saboda haka su ma akwai nasu bikin da su ke yi na kaɗe-kaɗe da bushe bushe irin na Fulani da ‘yan bori  wanda su ke ɗaukar tsawon wuni guda ana yi.

Bayan wannan a ranar biyu ga sallah ana ci gaba da bikin wanda a ka gudanar da rawar al’ ada wadda a ke kira da rawar taƙwai irin wannan rawa ce za ka ga mata da sanduna a hannun su suna rawa suna zagaya fage da sauran abubuwa na al’ada wanda jama’a da dama su ke halarta su cika garin. Domin za ka ga masu kiɗa da rawar al’ada rukuni rukuni kowa yana nuna tasa bajintar.

A ranar uku ga sallah kuwa an yi taron gudanar da waƙoƙi na zamani, wanda mawaƙa da dama suka halarta domin gudanar da na su bikin, wanda kuma a bisa tarihin masarautar wannan shi ne karo na farko da aka shirya waƙoƙi na zamani a cikin jerin shagalin bikin sallar da a ke yi.

Taron biki

Sarkin Ɗiyan Gobir (Dakta) Aminu Ladan Abubakar Ala shi ne ya jagoranci gudanar da waƙoƙin zamani tare da tawagar sa da suka tafi daga Nijeriya.

A wajen taron sun bajekolin waƙoƙin su na al’ada na faɗakarwa da yabon Manzon Allah SAW da waƙar Sarkin Gobir Sabuwa da Aminu Ladan Abubakar Ala ya gabatar kuma na soyayya, wanda kuma shi ne ya kawo ƙarshen jerin bukukawan Ƙaramar Sallar da aka shirya na wannan shekara, kuma ya samu halartar ɗimbin mutanen da aka daɗe ba a samu kamar sa ba.

An dai yi bikin an ƙare lafiya da fatan Allah ya kai mu ta shekaru masu zuwa.