Jakadan Sin ya yi kira a bada fifiko wajen bunƙasa cigaban yankin Sahel

Daga CMG HAUSA

Wakilin ƙasar Sin ya buƙaci a bada fifiko wajen bunƙasa cigaban yankin Sahel. Zhang Jun, zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD, ya ce Afrika tana fuskantar wahalhalu wajen cimma nasarar samun cigaba. Matsalolin ƙarancin abinci da duniya ke fuskanta a halin yanzu, da matsalar makamashi, da ta kuɗaɗe, sun kara tsananta halin da ake ciki a Afrika, sannan matsalar ta fi kamari a yankin Sahel.

Zhang Jun, ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin sulhun MƊD game da shirin G5 Sahel, wato wani shiri ne na hadin gwiwa don tsara manufofin bunƙasa cigaba da tabbatar da tsaron yammacin Afrika.

Jakadan na ƙasar Sin a MƊD ya bayyana cewa, MƊDr tana shirin tsara muhimmin shirin bincike na hadin gwiwa tare da ƙungiyar tarayyar Afrika AU, da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika wato (ECOWAS), da yankin Sahel. Ya ce ana fatan MƊD za ta ƙarfafa tuntuɓar juna tare da dukkan masu ruwa da tsaki wajen cimma wannan shiri, da nufin zurfafa goyon bayan juna, da haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen shiyyar.

Da yake ƙarin haske game da haɗin kai da haɗin gwiwa, Zhang ya ce, babu wata kasa da za ta iya magance waɗannan ƙalubaloli ita kaɗai. Ya kamata ƙasashen shiyyar su ƙarfafa goyon bayan juna, da haɗin gwiwa, tare da tallafin ƙasa da ƙasa, domin fito da matakan tinkarar matsalolin ta hanyar haɗin gwiwa.

Mai Fassarawa: Ahmad Fagam