Kaso 30 na marubuta kawai ke buga littafi – Umar Muhammad

“Zuwan wayoyin zamani ne ya girgiza kasuwar littafai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Satar fasaha na daga cikin manyan matsalolin da marubuta a ko’ina a duniya ke fama da su, idan ana batun ƙirƙira, rubutu, da adabi. Marubutan adabi ma suna fama da nasu irin ƙalubalen da ke dakushe cigaban harkar rubutun adabi. Fitowar sabuwar manhajar zamani ta ArewaBooks ta zo a lokacin da ake buƙata, sakamakon yadda take ƙoƙarin killace rubuce rubucen littattafan Hausa, musamman na yanar gizo, don masu karatu da kasuwancin littattafai cikin tsari da kiyaye haƙƙin mallakar marubuci. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu ya zanta da Malam Umar Muhammad, matashi mai nazarin ilimin na’urar sadarwa ta kwamfiyuta, wanda ya ƙirƙiro da wannan manhaja, domin jin manufar sa da yadda wannan tsari zai ceci harkokin adabi.

MANHAJA: Zan so ka gabatar mana da kan ka?
UMAR: Sunana Umar Muhammad. Ni haifaffen garin Minna ne, da ke Jihar Naija. Na fara karatuna a makarantar firamare ta Chiroma da ke cikin garin Minna, amma ban kammala a nan ba sai aka mayar da ni wata firamare ta kuɗi, in da na ƙarasa shekaru biyu a nan. Na shiga makarantar sakandiren gwamnati ta GSS Minna, a nan ma dai ban kammala ba aka mayar da ni wata makarantar mai suna Father O’Connell Science College, a nan na kammala a shekarar 2019. Daga nan na nemi shiga makarantar Sa’adatu Rimi College of Education (SRCOE) Kano, inda nake nazarin ilimin na’urar Kwamfiyuta da Lissafi a matakin NCE 3. A ɓangaren karatun addini kuma na yi karatun Al-ƙur’ani a makarantar Malam Garba Zabo dake Unguwar Limawa a garin Minna, a shekarar 2015 kuma Allah ya nufe ni da sauke Alƙur’ani mai girma. 

Wacce gwagwarmaya aka yi a fagen neman ilimi?
A fagen neman ilimi, yayana Salisu muna ce masa Big Bro, shine wanda ya ɗauki nauyin karatuna daga matakin firamare da sakandire, haka ma har walimar saukar Alƙur’ani da na yi. A waxannan matakan duk ban fuskanci wani ƙalubale ba. Amma inda gwagwarmayar take shine, tafiyata karatu Kano, duk da muna da irin wannan makarantar a garinmu, amma na zaɓi in tafi Kano. Da kaina na binciko makarantar a yanar gizo. Da farko yayana bai amince ba, amma ganin na ƙi haƙura haka ya sa ya amince.

Sai bayan da na yi kwana biyu a makarantar ne, na ga Kano kuma Kano ta ganni, sai na fara kuka da zaɓin da na yi, ina tambayar kaina “mai ya sa na zaɓi in zo Kano bayan ga gida inda zan huta?” Ban samu amsar da na iya bai wa kaina ba sai a lokacin, da na kammala manhajar Hausa Bookstore na samu amsar tambayata.

Shin ka na rubutun littafi ne kai ma, kuma littattafai nawa ka wallafa?
A’a, ni ba marubuci ba ne, amma makaranci ne. Ko da yake ina da sha’awar yin rubutun nan gaba.

Ba mu labari kan yadda ka samar da manhajar Arewa Books?
Wato tunanin samar da “ArewaBooks” ya fara samo asali ne a cikin watan Janairu na 2021. Ni makaranci ne, kamar yadda na faɗa a baya. Wata rana ina cikin karatun wani littafi da ake tura wa ta manhajar WhatsApp a zauruka daban daban, sai naci karo da wasu kalamai da ke cewa, “Wannan littafin na kuɗi ne, duk wanda ya karanta bai biya ba, Allah ya isa.” Abin da ya ban mamaki kenan tare da dariyar abin da wannan marubuciyar ta rubuta. Domin a lokacin yadda littattafan Hausa ke yawo a yanar gizo sakaka babu tsari wallahi a tunanina duk a kyauta ake rubutun su. 

Za ka rika ganin su a zaurukan Facebook zuwa Wattpad, wasu kuma su buxe zauruka a whatsApp suna yaɗawa. A lokacin ina cikin wasu irin waɗannan zaurukan da kullum sai an turo da littattafai ta documents. Na tara aƙalla littattafai fiye da dubu 2. Amma cin karo da “Allah ya isa” din nan ya canza min tunani. Hakan ya sa na fara bincike a kai.

Bayan wani lokaci na gano abubuwa da dama akan harkar rubutun littattafan Hausa, kuma a cikin kaso ɗari na marubuta, kaso 70 cikin ɗari suna rubutu ne a manhajojin Wattpad, WhatsApp da kuma Facebook, sai kaso 30 cikin ɗari su ne masu buga littafi.

A bincikena na gano marubutan WhatsApp su ne masu littafin “Allah ya isa”, matsalar shi ne masu bibiyar littattafan nasu suna fitar da su ne, ta wani ɓangare kamar masu Bloggers, sannan ga masu zaurukan WhatsApp da Facebook da ke tura wa mutane suna karɓar kuɗi ba tare da sanin marubutan ba.

Daga lokacin na fara tunanin mene ne mafita? Kuma da yake lokacin ina koyon yadda ake tsara manhaja ne a na’ura mai ƙwaƙwalwa wato programming, sai na fara tunanin na samar musu da wata manhaja ta marubutan Hausa kamar yadda ýan kudu suke da manhajar Okadabooks. 

Farkon aikin da na fara shine, Hausa Bookstore a cikin watan Yuli, na shekarar 2021. Bayan na kammala, sai na fara cin karo da ƙungiyar marubuta ta “Arewa Authors Forum” (AAF) inda suka gayyaceni taronsu, sun kuma karɓe ni hannu bibbiyu. A nan na kaddamar da manhajata ta farko, Hausa Bookstore kuma marubuta sun bayyana farin cikinsu a kai har suka fara zuwa buɗe shafukansu, har wasu ma sun gwada saka littafinsu.

Ƙalubalen da na samu shine, sai mutane suka fara bayyana wasu ƙorafe ƙorafen su a kan tsarin manhajar, sai dai na ɗauki hakan a matsayin nasara ce, har na riƙa tuntuɓar marubutan ina jin ra’ayinsu kowa dai na faɗar albarkacin bakinsa. Da waɗannan bayanan na gane abin da marubutan ke buƙata, na haɗa su dukka, daga lokacin na fara tunanin sake sabon aiki wanda zai yi daidai da ra’ayin marubuta.

Mun fara aikin sabuwar manhaja a cikin watan Agusta, 2021 inda muka qaddamar da Arewa Books a ranar . A ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 2021, a taron ƙungiyar marubuta ta ANA reshen Jihar Kano da ta gabatar a wannan watan.

Wanne cigaba wannan Manhaja za ta kawo ga cigaban adabi da kasuwancin littattafai?
In sha Allah manhajar ArewaBooks za ta kawo cigaba ga littattafan adabi a yanar gizo , zai zama kowanne marubuci yana da cikakken Haƙƙin Mallakar littattafansa. Kuma zai kawo ƙarshen ɓacewar littattafai, da yawa akwai waɗanda sun yi rubutu tun shekarun baya, amma yanzu idan za ka tambaye su su kansu ba su san inda za su same su ba.

A ɓangaren kasuwanci kuwa, ArewaBooks tamkar kasuwa ce, inda duk wani marubuci ke da damar baje hajarsa don masu bibiyarsa su saya cikin natsuwa. Sannan kasancewarsa kasuwa zai zama dandali ga makaranta, yadda za su iya ganin wasu littafan har ya burgesu su saya. Kuma ta dalilin hakan sabbin marubuta za su iya samun karɓuwa tare da nuna tsantsar basirarsu idan sun fitar da littafi mai jan hankali.

Mene ne ya bambanta Arewa Books da sauran manhajoji na tallata littattafai irin su Okada Books?
Tabbas lokacin da nake kan bincikena na bi ta kan Okadabooks, kusan duka littattafan da ke ciki na turanci ne, ka ga kenan harshen da ya fi ƙarfi a ciki ba irin na ‘yan Arewa ba ne. Don haka muka samar da wannan manhajar, da za ta dace da al’ummar Arewa. Sannan muna da bambancin tsarin kasuwancin littattafai da su, wanda sai wanda ya yi amfani da duka biyun ne zai gane hakan.

Wanne ƙoƙari kuke yi na kare haƙƙin mallakar marubuci da kare shi daga masu satar fasaha?
Akwai tsaro da muka sanya a shafin mu na yanar gizo da manhajar mu. Sannan idan marubuci na son bai wa littattafansa tsaro na musamman muna da tsarin “App Only” wato saka littafi a Manhaja kaɗai ba tare da ya bayyana a shafin yanar gizo ba, ta wannan hanyar ba ya iya ɗaukar hoto ko screenshot din rubutun littafin. Sannan idan ma an yi nasarar sace littafin in dai a shafinmu za a ɗora, da zarar an yi ƙorafin abin da ya faru ta hanyar report daga cikin manhajar ko kai tsaye, za mu sauke wannan account din gabaɗaya. Idan ya kasance ba a shafin mu ba ne kuma mun tabbatar marubucin bai sake littafin a ko’ina ba sai a shafinmu to, tabbas kamfanin ArewaBooks zai yi ƙoƙarin bin diddigin wannan ɓarawo har ya shiga hannun hukuma.

Wacce shawara za ka ba marubuta dangane da rungumar wannan sabuwar fasaha ta yanar gizo?
Shawarata ga marubutan mu na Arewa da suke ganin zuwan fasahar yanar gizo ya lalata musu harkar buga littattafai shine, su sani suna kallon ɓangaren ƙalubalen ne kawai, amma idan su lura da cigaban da ake samu za su yaba sosai su ma. Tabbas za mu iya sarrafa yanar gizo yadda muke so da irin wannan manhaja ta ArewaBooks, zai zama softcopy yana killace a manhaja kamar yadda hardcopy suke killace a shagon sayar da littafai.

Idan iya buga littafi ka ko kike yi a sayar a kasuwa, mai zai hana ku buɗe shafi a ArewaBooks tare da karawa abun farashi, idan bugagge 1,000 ne to, na online na iya zama 1,500. Ka ga a haka sai makaranci ya zaɓa. Ko ba komai saka datar da mutum yake yi ba zai tashi a banza ba, tunda ana kasuwaci da shi gabaɗaya. 

Ka na ganin yanzu harkar buga littattafai ta zo ƙarshe kenan?
A’a, sai dai a gaskiya zuwan wayoyin hannu ƙirar Android ya girgiza kasuwar buga littattafai, ba ƙaramin tankaɗa ya yi wa kasuwar littattafan Hausa ba. Sai dai har yanzu akwai waɗanda sun fi jin daɗin masu amfani da bugaggen littafi wajen karatu, musamman marubutan.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?
Mahaƙurci Mawadaci.

Na gode.
Ma sha Allah. Ni ma Ina godiya.