Fa’idar Habbatus Sauda

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya:
Anti Bilkisu, mu na son mu san fa’idar Habbatus-Sauda.

Amsa:
Habbatus Sauda wata ƙwayar itaciya ce mai albarka, wacce ta ke tattare da fa’idoji kala-kala a jikin ɗan’adam wanda ya kamata dukkan iyali ya kyautu a ce suna ajiye ta a cikin gida domin magani da kariya ga iyali da kiwon lafiya.

Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye daban-daban saboda muhimmancinta da shahararta. Bayan sunanta Habbatus Sauda ana kiran ta Habbatul Baraka. Da Turanci kuma ana kiran ta da ‘Blessed Seed, Black Cumin, Nigella Aativa, Black Caraway’ da sauransu.

Daga cikin fa’idojin Habbatus Sauda akwai:
Magance larurar rashin ruwan nono ga mai shayarwa. Ga macen da ta haihu amma bat a da ruwan nono idan aka samu garin habbatus-sauda a zuba a madara mai ɗimi ta sha yana sa gudanar ruwan nono. Ko kuma a yi salalan garin hulba in an sauke a zuba zuma da garin habbatus sauda shi ma za a dace da yardar Allah. Wannan haɗi yana da muhimmancin gaske ga mata don inganta jikinsu da saukar da ni’ima.

Ga wanda garkuwar jikinsa ta yi rauni shan man habbatus sauda ko garinta a abinci ko abin sha ko a sha haka yana da matuƙar muhimmanci yana dawo da garkuwar jiki ta samu inganci.

Habbatus sauda yana da matuƙar amfani a rauni ko quraje musamman buɗaɗɗu. Bayan an tsaftace wajen. Ana shafawa a saman ciwon.

Ga wanda yake da ƙarancin maniyyi ana samun garin habbatus sauda cokali ɗaya babba a samu kwai guda biyu da farar albasa da tafarnuwa a yayyanka ta a saka a ciki a soya ƙwan sama-sama wato ruwa-ruwa a cinye zama ɗaya.

Ga wanda yake da matsalar da ta shafi fata kowacce iri ce ana amfani da man habbatus sauda da man zaitun da ma’uwardi a haɗe su wuri guda ake shafawa sau biyu a rana. In sha Allah za a samu sauƙi.

Za mu cigaba a mako na gaba in sha Allah.

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko ta WhatsApp 07088683334 ko a duba shafin Facebook ɗina mai suna Bilkisu Yusuf Ali.