Yadda baƙin al’adu a bukukuwa ke rusa tarbiyya

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi:
Babban tashin hankalin da ya tunkaro mu iyaye wannan na kowa da kowa ne, daga iyaye maza har mata, dole kowa ya nutsu ya gane gaskiya tun lokaci bai ƙure ba.

Game da harkokin biki na yaranmu, abun fa ya fara fita daga inda aka san yaran Hausawa, masoya addini. Tun daga gida muke rusa auren yaranmu. Maimakon ake shi musu albarka, yanzu ya koma tsinuwa ce take raka su ɗakin mazajensu. Wanda dai laifinmu ne iyaye mata da maza. Kowa yana da kamasho wajen jawo wa yaranmu la’antar mutane, ƙila ma har da ta Allah.

Me zai hana mu koma shigar suturunmu na gargajiya, mu ajiye wannan muguwar ɗabi’a da muka ɗauka rana tsaka muka ɗora wa kanmu da sunan wayewa? Kuma aƙalla idan an duba ba komai ya ja mana ba illa bin abun da yaranmu suke  so. Ba ma dubaiyya kawai sai mu bi son ransu mu bi su da hakan dai-dai ne.

Tun daga kan tambayar aure muka gama ɓata rawarmu da tsalle. Ƙarya ta baibaye jama’a kowa so yake a ce ‘yarsa ta samu miji mai hali.  Rayuwa ta riga ta canza idan miji ba zai kawo kayan ƙarya ba, to babu aure.

Lefe:
A da, daidai misali ake yi, amma yanzu ina! Sai an yi akwatuna saiti biyu ko uku. Ya ilahi, ina za mu kai wannan rayuwa? Dole kuwa yaranmu su rasa mazajen aure. Lefe a ce sai an sako a mota, an taho ana bidiyo ana gamawa a tura duniya ta gani? Wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare da sunan cinyewa. To wannan ƙauyanci ne da rusa rayuwa. Komai ya koma ba sirri, kowa sai ya gani. Don Allah iyaye mu yi wa kai faɗa mu gyara rayuwar yaranmu.

Ɗinkuna:
Bayan lefe, sai abu na gaba shi ne sabon salon wankan amarya. Shigar amare ba irin ta da ba ce, yanzu an canza da ɗinkin arna. Sannan a je a kama wajen biki da ƙawaye, ana raye-raye, ba laifi idan sun yi abinsu a gida. To yanzu sai an ɗauka an turo duniya ta gani. Yara sun baje surorinsu Duniya ta gani, har amaryar. Ango ya zama fanko, Duniya ta gama gane masa matar, meye abin jin daɗi cikin wannan saboda Allah? Wannan ba wayewa ba ce wallahi. Koma baya ne da koya wa yaranmu rashin sanin haƙƙin aure. Mu farka! Wallahi garin neman gira kada mu rasa ido.

Kayan da muke bari yaranmu suna sa tufafi na fidda tsiraici. Wallahi babu tsari babu kuma abun burgewa ciki, sai kiran ɓarna da fushin Allah. Yana da kyau mu kau da wannan mugayen ɗabi’u da muka ɗora wa kanmu. Duk wata shiga da arna suke muke gani a da muna zafinsu, ko muna jin kunya, to yanzu yaran musulmai sun ɗauka da gaske. Har sun fi arnan ma zaƙewa. Mu rufawa kanmu asiri mu bar son zuciyarmu, mu nunawa yaranmu gaskiya. komai suka yi, da sa hannunmu a ciki.

Mun bar al’ada:
Mun bar al’adar da muka gada iyaye da kakanni, mun ɗauki ɗabiar Nasara mun ɗora wa kanmu. Wanda mu iyayenmu ba haka suka yi mana ba, sun killace mu, sun suturta mu, mun je gidajen mazajenmu da daraja. Amma yau mun cuci yaranmu, mun tallasa su, mun tallata su a Duniya, mun kuma kai su fanko da sunan gata. Ya Allahu! Wallahi ba mu yi musu gata ba, don Allah mata mu farka.

Iyaye maza:
Gaskiya kun yi sake da yawa akan tarbiyyar yaranku. Anya kuna ganin yadda ake caccakar su a shafukan yanar gizo kuwa? Babban abun kunya ne wannan. 

Gayu:
Yayin da a da, muka ɗauki shigar Nasara matsayin gayu, to yanzu dai ta koma abun tur!  daman an ce kama da wane, ba ta wane. Saboda kowa da al’adarsa, kuma kowa da kiwon da ya karɓe shi. Meye laifin kayanmu na gargajiya ne? Dole sai mun aro rayuwar wasu mun ɗora wa kanmu? To yanzu dai ba mu da ikon da za mu zagi wasu, don mu ma dai ba mu da maraba da su cinyare da Ngozi. Abunda za su sa, mu ma yaranmu Shi suke sakawa. Allah ya sani laifin duk namu ne. Da ba mu goya wa yaranmu baya ba, da ba za su yi ba. Don haka, mu muka tarko wa kanmu magana.

Hotunan kafin aure:
To shi ma wannan wani salo ne na fitina kafin biki ango da amarya suke zuwa ɗauke-ɗauken hoto, daga nan sai a baza shi a Duniya. matsalar wasu hotunan sun mazanta, ba za ka taɓa cewa yaran Hausawa ne ba, masu kunya da gudun bakin Mutane. To yanzu ma ya za