Yadda mutuwar abokai ta fallasa taɓarɓarewar asibitocin Neja

Daga BASHIR ISAH

Mutuwar Sakataren Labarai ga Gwamnan Jihar Neja kuma tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Danladi Ndayebo, da ta Hadimin Shugaban Majalisar Dattawa, Mohammed Isa, ta fallasa irin taɓarɓarewar da fannin kiwon lafiyar jihar ke fama da ita.

Marigayan biyu sun rasu ne a sakamakon raunukan da suka ji a hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Minna zuwa Suleja.

Sai dai kuma, rahotanni sun ce sun mutu ne sakamakon sakacin ma’aikatan asibitocin da aka kai su da kuma rashin kayan aikin da za a kula da raunukan da suka ji.

Yayin da Danladi ya bar duniya ranar Litinin, shi kuwa Mohammed a Juma’ar da ta biyo baya ya ce ga garinku nan, duk dai a cikin mako ɗaya.

Wani ƙanin marigayi Danladi, Usman Mohammed Ndayebo, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, ɗan uwansa da kuma Mohammed ba su samu kulawar da ta dace ba a Asibitin Ƙwararru ta IBB da ke Minna, babban birnin jihar, har tsawon sa’o’i 13 bayan aukuwar hatsarin.

Ya ce, bayan sa’o’i huɗu da isa asibitin, wata allurar kashe raɗaɗin ciwo kaɗai aka yi musu don samun sassaucin zafin raunin da suka ji.

“Da misalin ƙarfe 9:30 na dare na isa Asibitin IBB inda na tarar babu wata kulawar da aka ba su. Ba da jimawa ba sai wani mutum ya shigo ya ce yana jira a kawo wasu magunguna da allurai ne. Bayan minti 30 sai ya zo ya yi masa wasu allurai don samun sauƙin raɗaɗin da yake ji.

“Bayan haka ba a sake bin ta kansu ba har zuwa safiyar washegari, duk da cikin dare sun koka game yadda suke. Da taimakon Farfesa Kuta Yahaya ne ɗan uwana ya samu kulawa da misalin ƙarfe 11 na safe.

“Mun fahimci cewa na’urar ɗaukar hoto (x-ray) da ta sikanin duk suna aiki, amma babu wani abu da aka yi in ban da in ban da ruwan da aka sa musu da kuma allurai. Albarkacin Farfesa Yahaya ne aka samu aka ɗauki hotonsu,” inji shi.

Mohammed ya ci gaba da cewa, daga bisani aka sanar da su akwai buƙatar a yi wa Danladi aiki.

“Bayan da likitoci suka zo da misalin ƙarfe 11 na safen washegari, suka faɗa mana cewa ɗakin ajiye masu buƙatar kulawa ta musamman (ICU) na Babban Asibitin Minna na aiki, don haka a ɗauke shi zuwa can don yi masa aiki.”

Ya ce, shi ma Mohammed wanda aka bari a nan Asibitin IBB, daga bisani an ɗauke shi zuwa Babban Asibitin Minna don ci gaba da ba shi kulawa.

Majiyar Daily Trust ta ce, an bar Mohammed ba tare da yi masa aiki ba har zuwa ranar Juma’a sannan aka ɗauke shi zuwa Asibitin Abuja bayan an yi masa aikin, duk da yanayin jikin nasa babu daɗi.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar wa Daily Trust cewa lallai ya samu rahoton kan cewa an bar wasu marasa lafiya mutum su biyu a asibiti ba tare da an kula da su ba.

“Da safen nan aka kira aka shaida mini cewa an ɗauki marigayi Ndayebo tare da wani mutum guda zuwa Asibitin IBB da daddare, amma da na kira da aka ce mini babu likita ko dayan da zai duba waɗanda suka yi hatsarin.

“Sai washegari da safe aka duba shi, sannan bayan wani ɗan lokaci ya ce ga garinku nan,” inji Matane.

Ya ce gwamnati ta damu matuƙa da faruwar irin wannan sakaci a asibitinta wanda ya kamata a ce mara lafiya na samun kulawar gaggawa a kan lokaci.

Ya ci gaba da cewa, an kafa kwamiti a bisa umarnin Gwamna Abubakar Sani Bello, domin gudanar da binciki tare da gano musabbabin mutuwar Ndayebo.

Sai dai kuma, binciken Daily Trust batun Ndayebo da Mohammed kaɗan ne daga cikin masu yawan da suka auku.

Domin kuwa, an shafe shekara marasa lafiya na mutuwa a asibitocin jihar saboda rashin likitoci da ma’aikata.

Sakamakon bincike ya nuna marasa lafiya da daman gaske, ciki har da mata masu naƙuda suke rasa rayukansu a asibitocin saboda rashin ma’aikata, musamman irin marasa lafiyan da akan kawo magashiyan masu buƙatar kulawa ta gaggawa.

Daily Trust ta tattaro cewa, a wasu asibitocin jihar, jami’i ɗaya tak ake wakiltawa ya duba masara lafiya sama da 20 da daddare bayan ‘yan likitocin da ake da su sun tashi aiki.

Idris Mohammed ya bayyana cewa, ya taɓa samun hatsari inda aka ɗauke shi zuwa Babban Asibitin Minna, sai dai bai ji da daɗi ba.

“Na tuna, an ce mu sayi safar hannu, na kuma saya. Amma sai da aka shafe sa’o’i masu yawa kafin jami’ai suka taɓa jikina. Sannan sai bayan kwana biyu kafin na ga likita. Duk lokacin da ‘yan uwana suka tambaya game da likita, sai a ce musu lambar wayarsa ba ta shiga ko da an kira,” inji shi.

Wani magidanci mai suna Mr Nathaniel Sunday, wanda aka taɓa yi wa ɗansa aiki a ciki a Babban Asibitin na Minna, ya shaida wa Daily Trust cewa, ma’aikatan da ke duba marasa lafiyar da aka kai aisibiti masu buƙatar gaggawa, ɗalibai masu neman sanin makamar aiki akan bai wa su duba su.

“Hatta likitocin ma haka suke ke. Ba muna nufin kada su koyi aiki ba ne, amma ba daidai ba ne a sakar musu komai,” inji shi.

Sunday ya ce, ƙwararrun likitocin da ke ɗakin da ake ajiye waɗanda suka samu hatsari da ɗakin masu buƙatar gaggawa, ba su zuwa duba marasa lafiya yadda ya kamata, sannan ƙwarrarun nas-nas da ake da su, su kuma umarni kawai suke bai wa ɗaliban da aka turo masu neman sanin makamar aiki.

“A ce wai, mara lafiya da aka kawo asibiti hajaran majaran, an bar shi a hannun ɗalibai su duba shi, wannan ba daidai ne ba,” inji Sunday.

A bayyane yake cewa, ƙarancin likitoci da sauran ma’aikata, haɗi da rashin wadatattun kayan aiki, su ne manyan matsalolin da suka addabi asibitocin Jihar Neja.

Shugaban Ƙungiyar Likitoci na Ƙasa reshen Jihar Neja, Mohammed Yusuf, ya tabbatar da ana fama da ƙarancin ma’aikata a asibitocin jihar.

Haka shi ma Kwamishinan Hukumar Kula da Asibitocin Jihar, Dakta Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar lallai akwai wannan matsalar.

Amma da aka nemi jin ta bakinsa, Kwamishin Ma’aikatar Lafiya na Jihar, Dakta Mohammed Makusidi, ya ce wannan matsala ba a kan Jihar Neja kaɗai ta taƙaita ba, amma matsala ce da ta shafi ƙasa baki ɗaya.