Buhari ya amince da ƙarin albashi wa ma’aikatan shari’a

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince tare da ba da umarnin gaggawa game da aiwatar da ƙarin albashi ga ma’aikatan fannin shari’a.

Buhari ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen bikin buɗe wani sashe na Makarantar Lauyoyi a Fatakwal.

Hadimin Babban Lauyan Ƙasa kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Dakta Umar Gwandu, shi ne ya bayyana haka.

Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, shi ne ya wakilci Buhari a wajen taron.

A cewar jaridar Punch, Buhari ya buƙaci Hukumar Tara Kuɗin Shiga da Rabawa da kuma Ministan Shari’a da su haɗa kai su yi nazarin yadda ƙarin albashi ga ma’aikatan fannin shari’ar zai kasance.