Rikicin gwamnati da ASUU na neman ƙara rincaɓewa

*An ɗage zana jarrabawa a Kano
*”’Yan takarar Shugaban Ƙasa biyu na shirin cefanar da jami’o’I”

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta dage cewa ba za a biya malaman jami’o’i albashin aikin da ba su yi ba, daidai da manufar ‘ba aiki, ba albashi’.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, ranar Laraba, 16 ga Nuwamba, 2022.

Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a 16 ga watan Oktoba, 2022, ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta shafe watanni 8 tana yi, wadda ta rufe jami’o’in gwamnati a ƙasar nan, domin neman cikakken aiwatar da yarjejeniyoyin da ta ƙulla da gwamnatin tarayya a shekarun baya.

Yayin da yajin aikin ASUU ya ci tura, gwamnatin tarayya ta dage kan aiwatar da manufar ‘Ba A Aiki, Ba Biya’ a lokacin da malaman jami’o’in ba su yi aiki ba.

Sai dai al’amura sun sake ɗaukar sabon salo a ranar Alhamis zin da ta gabata, 3 ga Nuwamba, 2022, inda aka tattaro cewa gwamnati ta biya malaman jami’o’in albashi na rabin wata ne kawai.’ ASUU ta kuma shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar.

A ɓangare guda kuma, Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sake ɗage duk wasu ayyukan ilimi da suka haɗa da jarabawar da za a yi a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022, biyo bayan wa’adin da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ayyana na zanga-zanga.

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na BUK Bala Abdullahi ya sanya wa hannu a madadin magatakardar ya bayyana cewa, an ɗage ayyukan karatun.

An shirya gudanar da jarrabawar ne daga ranar 17 ga Nuwamba zuwa 8 ga Disamba, 2022.

A cikin sanarwar da aka buga a cikin sanarwar jami’ar, hukumar ta sanar da jami’o’i da sassan da abin ya shafa game da buƙatar gaggawa.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ASUU reshen BUK, Dr. Sagir Saleh, ya shaidawa jaridar Guardian cewa, ƙungiyar ta yanke shawarar yin zanga-zanga tare da ayyana ranar da babu shiga aji domin nuna rashin amincewa da albashin da aka yanke wa mambobin ƙungiyar na watan Satumba.

Saleh ya dage cewa, ASUU ta fara zanga-zangar ne a matsayin gargaɗi kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar sabbin matakan da ka iya cutar da tsarin.

Ya ce, ASUU za ta yi amfani da wannan dama wajen miƙa takardar zanga-zangar ga mataimakin shugaban ƙasa domin miƙawa ministan ilimi.

Bashir ya jaddada cewa, duk da cewa ’ya’yan ƙungiyar ta NAMDA sun sha wahala daga gwamnatin tarayya, shiga duk wata fafutuka da ASUU zai ƙara dagula lamarin.

Ya ce:, “ba za mu yi wata zanga-zanga da ASUU ba saboda ba mu cikin ƙungiyar malamai ɗaya. Muna da al’amuranmu na musamman kuma mun gwammace mu magance matsalolinmu a hanya daban.

A ɗaya ɓangaren kuma,  Shugaban ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa, ’yan takarar shugaban ƙasa biyu na shirin sayar da jami’o’in gwamnatin tarayya ta hanyar haɗin gwiwar jama’a masu zaman kansu.

Osodoke ya bayyana hakan ne a wani taro ranar Juma’a a Markurdi, babban birnin jihar Benue.

Koda yake ya kasa tantance ’yan takarar shugaban ƙasar biyu, amma ya ce, suna da shirin mayar da jami’o’in mallakar gwamnati zuwa na masu zaman kansu.

Ya ci gaba da cewa, nan ba da jimawa ba ’yan takarar shugaban ƙasa za su fito da tsare-tsare na mayar da jami’o’in gwamnatin tarayya hannun jari ta hanyar sayar da su.

Da ya ke magana a kan jami’o’in Nijeriya da ke karɓar lamunin ɗalibai, shugaban ASUU ya ce, “a Nijeriya inda kuke da waɗanda suka kammala karatunsu da ba za su iya samun aikin yi ba na tsawon shekaru da yawa kuma idan kun shafe shekaru 30 lamunin zai kai Naira miliyan 40.”

“Bayan mun gama da gwamnatin tarayya, za mu dawo kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗe a jami’o’inmu saboda wasu jami’o’in na da matsalar rashin sarrafa kuɗaɗe.

“A matsayinmu na jami’a, ba mu san yadda ake kashe kuɗi ba, jami’o’in nawa ne ke da kasafin kuɗi. Gwamnatin tarayya, majalisun ƙasa na da kasafin kuɗinsu amma ba haka ya ke ba a wasu jami’o’i ba. Za mu yi yaƙi da hakan nan ba da jimawa ba,” inji Osodeke.