Yadda ’yan siyasa ke jefa matasa bangar soshiyal midiya!

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ana ci gaba da samun sauye-sauye a harkokin siyasa a ƙasar nan, yayin da ake ƙara kusantar Babban Zaɓe na shekarar 2027. ‘Yan siyasa, musamman sabbin yanka masu neman a san da su da gwamnoni masu neman tazarce suna ta ƙoƙarin sauyin sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Mun ga yadda jihohi irin su Kano, Filato, Adamawa, Taraba da Zamfara gwamnoninsu suka yi sauyin jam’iyya zuwa babbar jam’iyya mai mulki ta APC. Matakin da wasu ke kallo a matsayin wayon a ci ne, wato kowa ƙoƙari yake yi a dama da shi a siyasar tarayya, a sha romon dimukraɗiyyar tare da shi. Kodayake akasari suna faɗin cewa sun yi canjin sheƙar ne don maslahar jihohin su, da cigaban al’ummar ta. Kamar misalin Jihar Zamfara da gwamnanta ya kasance na baya-bayan da ya yi sauyin sheƙa, wanda kuma ya bayyana hakan da ya yi don samun cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya ne kan sha’anin tsaron jiharsa.

A yayin da muke daga gefe muna nazari kan sabbin sauye-sauyen da ake samu a ƙasar nan, da yadda siyasar ke ƙara ɗaukar sabbin salo, wani ɓangare da yake ɗaukar hankali shi ne kafafen sadarwa na zamani musamman zaurukan sada zumunta, inda ’yan siyasa suka raja’a wajen karkatar da hankalin ’yan ƙasa zuwa ga ra’ayoyinsu da fahimtarsu. Amfani da ’yan jagaliyar siyasa a manhajoin WhatsApp, Facebook, Tiktok da Instagram na cigaba da haifar da rabuwar kai da ruɗani a tsakanin ýan Nijeriya. Sun kasa tantance alƙiblar da za su fuskanta, saboda yadda kowa ke nuna ɓangarensa ne yake kan daidai. Yayin da a wasu jihohin ma har da ɗaukar nauyin matasa masu rubuce-rubuce na ɓata suna da yaɗa ƙarairayi, don dakushe farinjinin abokan adawa. Ba ’yan siyasa kaɗai ba har ma da jami’an tsaro, hukumomin gwamnati, ’yan kasuwa da kuma sarakuna.

Kowa ya zama ɗan siyasa, ko mai sharhi akan harkokin siyasa, saboda yana da babbar waya, yana ganin yana da damar bayyana duk abin da ya ga dama, ba tare da la’akari da tasirin da hakan zai yi a rayuwar sa da al’ummarsa ba. 

’Yan siyasa na amfani da waɗannan matasa ne saboda jan hankalin sauran jama’a su fahimci tsare-tsaren su da manufofinsu na siyasa, musamman kasancewar matasan su ne suka fi mu’amala da waɗannan shafuka, sakamakon yadda akasarin waɗannan matasa ke zaune babu ayyukan yi, ko babu wasu nauye-nauye a kansu da za su ɗauke musu hankali.

A baya mun ga yadda ’yan siyasa suka riƙa amfani da matasa wajen ba su kayan shaye-shaye suna yi wa kansu illa da sunan bangar siyasa, ana tura su tarwatsa cibiyoyin zaɓe, satar akwatin zaɓe da kisa ko yi wa abokan adawa lahani. Mun ga yadda ’yan jagaliyar siyasa a Kano, da ’yan Kalare a Gombe, ’yan Gunda a Bauchi, da ’yan ECOMOG a Borno suka haifar da babban ƙalubalen tsaro a jihohinsu, wanda har yanzu ba a kammala warware su ba. 

Za a iya cewa, wannan salo na amfani da soshiyal midiya ya kawo sauyi a harkar jagaliyar siyasa, inda yanzu harkar ta koma bayan fage ake yin ta a wayoyin hannu ba tare da makami ko shaye-shaye ba, sai data. Kamar yadda wasu ke cewa, alƙalami ya fi takobi kaifi, tabbas haka ne. Amfani da kalaman ɓatanci, cin zarafin juna, da yaɗa labaran ƙarya don lalata kima da mutuncin wani ɗan siyasa ko abokin adawa, ita ma illa ce babba, da ke da haɗari ga ci gaban al’umma da zaman tare. 

Babu wani ɗan siyasa a yanzu da za ka ga ba shi da wasu rukunin matasa da ya ware yana basu wasu ’yan kuɗaɗe suna sayen data don taimaka masa wajen yaɗa manufofinsa, inda kuma za ka ga wani lokaci har da tayar da muhawara mai zafi tsakanin magoya bayan wannan ɗan takara zuwa wancan. Kowanne ɓangare na fifita ɗan takarar da suke goyon baya, ko dai saboda wasu ayyuka da ya yi wa jama’a a baya na cigaba, ko yawan muƙaman da ya riƙe a baya da gogewarsa, ko yadda yake nuna kishin sa ga jama’ar yankinsa, addininsa ko tallafawa matasa da ayyukan yi. 

Waɗannan na daga cikin abubuwan da akasari aka fi amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe a zaurukan sada zumunta. Kuma hakan a ra’ayin wasu matasan ’yan siyasa yana tasiri sosai, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu, musamman idan aka yi dace da gwanayen iya rubutu da mayar da martani ga duk wani motsi na abokan adawa, wanda kuma yake da mabiya ko abokai da dama, ta yadda da zarar ya tura saƙo ɗaya cikin ’yan mintina ƙalilan zai jawo muhawara da tattaunawa a kai. 

Usman Bigi yana daga cikin matasan da suke wannan aiki na siyasar soshiyal midiya, ya kuma bayyana min cewa babu shakka ana samun alheri kadaran-kadahan, amma yawanci matasa sha’awa ce take kai su ga shiga wannan harka saboda suna son su ma a riƙa damawa da su, musamman a yayin da aka shiga kakar zaɓe, don kada a yi babu su. 

Shi kuwa Bala Sawaba matashin ɗan siyasa ne da kodayaushe za ka same shi a gidan wannan ɗan siyasa zuwa wancan, yana abin da ake cewa Kala, shi da wasu abokansa, don samun na sayen data, da shiga cikin manyan ’yan siyasa ana tattauna hanyoyin cin nasarar zaɓe da nakasa tasirin abokan adawa. A ganin sa duk wani matashi da yake da burin yin siyasa to, dole ne ya zama yaron wani, don ya koyi dabarun siyasa, ya samu gogewa kuma a san shi sosai a harkar. 

Ummu Ayman matashiya ce da ake gogawa da ita a wannan fage a cikin mata ƙalilan da suke ba da gudunmawa wajen muhawara kan ‘yan siyasa a zaurukan sada zumunta ta yi fatan ‘yan siyasa ba za su manta da su ba bayan samun nasarar zaɓe, domin yabawa da irin rawar da suka taka. A maimakon ko da yaushe a bar su da tura mota tana tashi ta buɗe su da hayaƙi, ba za a sake waiwayar su ba sai wani zaɓen ya zo. 

A dalilin haka ne, wani matashin ɗan siyasa a Jos, Malam Abdulhadi Abdullahi ya fito da wani salon jan hankalin matasa inda yake kiran matasa masu siyasar soshiyal midiya su tabbatar sun mallaki katin zaɓen su a hannu, domin ranar zaɓe su yi amfani da shi wajen kawo sauyin da suke da burin gani a siyasar yankin su. Kuma da alamun wannan salo nasa yana samun karɓuwa, a wajen wasu matasan. 

Masu hikimar magana dai na cewa, zamani riga ne. Allah kuma shi ne zamani. Babu wanda zai yi faɗa da abin da zamani ya kawo, amma kuma ba zai yiwu a yi shiru a kawar da kai ba, akwai buƙatar matasa su samu jagoranci da saiti kan yadda za su tafiyar da wannan harka ta soshiyal midiya da kaucewa haɗarinta. Don ya kasance ba a fagen siyasa kaɗai ba har a sauran harkokin su na rayuwa zai zama musu mai amfani. 

A lokaci guda kuma ya zama wajibi a tunatar da matasa cewa, Facebook ko ɗ da WhatsApp ba jam’iyyun siyasa ba ne, kuma ba katin zaɓe ko rumfar zaɓe ba ce, dole in suna buƙatar yin siyasa sosai, su je su yi rijista da wata jam’iyyar siyasa da suka aminta da tsarin ta da manufofin ta, kuma su tabbatar suna da katin zaɓe a hannun su, don ya zama makamin su na kawo sauyi a al’amarin rayuwar su da al’ummar su. 

Sannan kuma su tabbatar sun koma makaranta ko kuma sun kammala karatunsu, ta yadda ko da taimaka musu wani ɗan siyasa zai yi, zai yi musu taimakon da zai inganta rayuwar su ne, wajen sama musu aikin da ya dace da wahalar da suka yi masa ta yaƙin neman zaɓe, masu sana’o’in dogaro da kai kuma su dage wajen riƙe sana’o’in su, da mutunci, kada su bari siyasa ta ɗauke musu hankali daga abin da yake tsare mutuncin su, da tallafawa iyalan su. Domin duk wani abu da za su samu daga wani ɗan siyasa, ba wani abu ne da ya kai ya kawo ba. 

Harwayau kuma, ina mai ba da shawara, a yayin da ake tattaunawa game da gudunmawar ýan siyasa a riƙa kawo batutuwa masu muhimmanci da za a riƙa ƙalubalantar ’yan siyasa a kai, abubuwan da za su kawo wa al’umma ci gaba da makoma ta gari. A maimakon a yi ta zuga su ana yabawa ayyukan da suka yi na neman suna ko son a sani, ba na tsakani da Allah ba, a mafi akasarin lokuta! 

A kaucewa rubuce rubuce-rubucen hassala juna ko tsokano fitina don a ci zarafin wani ko aibata shi. Abin da ka iya haifar masa da mummunan suna da lalata mutuncin sa ba kawai a siyasance ba, har ma da martabar sa a idon al’umma da ta iyalansa.

By ukarofi