Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Tun sauya sheƙar Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara daga PDP zuwa APC na zuba ido ko zan ga wani ɗan zilla ya yi fatar alheri cewa Allah ya sa manyan Zamfara su haɗa kai don salamar jihar, sai shiru tsit ka ke ji. Ba ma kawai rashin addu’ar alheri ba, yanzu idan ‘yan zilla za su lissafa manyan ‘yan siyasar da su ka yi wa rejista a farafagandarsu, ba sa ambatar sunan gwamna Dauda! Shin hakan ya damu gwamnan kuwa? Ba na tsammani don ko a suɓutar baki ba mu taɓa jin ya ambaci sunan ‘yan zilla ko nuna akwai wani bambanci a tsakanin al’ummar jihar Zamfara ba, maganarsa ita ce ba zai tattauna da ‘yan ta’adda ba don ‘yan ta’adda ‘yan ta’adda ne, ba a tantance su da addini ko wata keɓantacciyar ƙabila.
Daf da haɗuwar manyan ‘yan siyasar biyu daga Zamfara a jam’iyya ɗaya, ‘yan zilla sun kanbama Dauda da cewa shi ne irin gwamnan da a ke buƙata, ga kyau ga aiki ga shi ɗan zalla a wajensu! A lokaci guda su ka taƙarƙare ga kamfen ɗin lallai sai shugaban ƙasa ya cire ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle daga muƙaminsa. Lissafin dai ya canja ko a nan za a gane mutanen nan ba sa son Arewa ta zauna lafiya don duk inda su ka ga an gaisa a na neman hanyoyin maslahar tsaro, sai baƙin ciki ya kama su, su kauce. Sun kyale gwamna Dauda ba su yi ta surfa ma sa ashar ba don jerin gwanon yabo da su ka yi ma sa ba zai yiwu su yi ribas da giya ɗaya ba, sai a hankali za su janye su ɓullo da wata fitinar don kar a taɓa samun zaman lafiya a jihar Zamfara.
Tsohon gwamna Bello Matawalle ya marabci Gwamna Dauda zuwa jam’iyyarsu da nuna tamakr dama ai “…He is my brother..” don haka ma Matawalle ya jingine batun shirin sake neman takara a 2027 don marawa burin Dauda na tazarce baya. In kun lura dama hamayya ce ta siyasa a tsakaninsu amma ba kamar surutan ‘yan zilla ba da ke neman kunna fitanar ƙabilanci a jihar don haddasa fitanar da ba za ta kare ba sai sun samu nasarar murƙushe tasirin Hausawa, Arewa da Musulunci.
Ginshiƙan zaman Dauda gwamna a fili su ke kuma ciki har da yadda Matawalle ya sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan ya taɓa alwashin ba zai bar PDP ba. Sai kuma hakan ya sa lallai sai ya takurawa mataimakinsa Mahdi Aliyu ya dawo APC ko su tsige shi. Haka dai Mahdi ya ki yarda don haka su ka tsige shi da naɗa Sanata Hassan Nasiha Gusau a kujerar. ƙungiyar ‘yan G8 wato manyan ‘yan siyasar Zamfara duk su ka dawo APC a ka bar Dauda a PDP kuma Allah ya ba shi nasara ba a doron ƙabilanci ba sam-sam. Na yi magana da Dauda a lokacin ya shaida min ya gode Allah da ya haɗa ma sa duk gaggan ‘yan siyasar a gefe daya sannan ya ba shi nasara. Duk yunƙurin ture nasarar Dauda ta ci tura, haka ya zama gwamna. In zunubi ne sauya sheka daga PDP zuwa APC to wa zai tsira a cikin biyun? In zama a PDP ne ke tabbatar da tsaro a Zamfara, yanzu duk sun dawo APC sai kaka kenan? Masu farafaganda sun ji kunya don rashin jituwar siyasa da ma rashin tsaro a Zamfara ba batun ƙabilanci ba ne, fitina ce da ya dace kowa ya ajiye bambancinsa a yake ta da kuma neman taimako daga Allah. Dama yaya za a yi wanda bai yarda da Arewa ko addinin Hausawa ba ya goyi bayan maslaha? An yi babbar walƙiya wal-wal an ga mutanen da ba sa son salama.
Duk mai nazari zai ga lamarin nan filla-filla kamar zanen tafin hannu yadda Yammawa su ka daɗe su na ƙulle-ƙulle lallai sai sun kai Nijeriya kasa ko ta halin kaka. Hasashensu na baya-bayan nan shi ne na wargajewar Nijeriya a shekara ta 2015 amam cikin ikon Allah kasar ta tsallake har ga shi ta shekara 11-12 ta na nan ko ma dai ba daram ba. Mun tuna yadda ta faru a 1967 inda ‘yan awaren Biyafara su ka balle daga Nijeriya. Nan take wata kasar jan kunne ta mara mu su baya. Dakaru daga Arewa su ka bazama don hade Nijeriya. In ka ji a na batun Nijeriya to Arewa a ke magana shi ne kashin bayan Nijeriya. Jajircewar dakarun nan na Arewa irin su Janar Hassan Usman Katsina, Janar Yakubu Gowon, Janar Theophilus Danjuma, Janar Murtala Muhammed, Janar Mamman Shuwa, Janar Muhammadu Buhari, Janar Ibrahim Babangida da sauran manyan dakka, a ka samu nasarar dinke kasa daya, ya zama babban zunubin da Arewa ta yi wa Yammawa kuma har yau ba su yafe ba.
Gaskiyar magana lura da Arewa ita ce Nijeriya shi ya sa Yammawa waɗanda tun ma zamanin mulkin mallaka su ka yi yunƙurin mayar da kowa mabiyin ɗabi’unsu, amma hakan ya ci tura, sai su ke ɓullo da hanyoyin wargaza Arewa don ta nan ne za su samu damar murƙushe Nijeriya. Haƙiƙa da zarar Nijeriya ta faɗi to tabbas Afurka ta baƙaƙen fata ta shiga garari inda kullum labarun da za su ke fitowa su ne na cututtuka, miyagun kwayoyi, ‘yan tawayen ƙabilanci da gano manyan kaburbura tamkar yadda ya kasance a Rwanda da kuma Saliyo da duk mai labarin Fode Sanko mai gille hannun hatta jariri don kar ya zama mai amfani.
In tun kafin ma Bishop Wilfred ya kai labaru wajensu Riley Moore, akwai ayyuka na ƙarƙashin kasa na dasa nakiyoyi don wargaza Arewa. ɓarayin dajin nan da su ka samu horo daga ‘yan aware na daga makircin da a ka ƙulla. Lura da yadda Arewa ke zama ginshiƙin addinin Musulunci da kirista a duniya ya sa biyowa ta doron addini don hargitsa yankin. Duk jagororin kamfen ɗin bazata ba musulmi ba ne kuma dama sun tashi da tarbiyyar kin jinin Musulunci.
A nan duk wanda bai fahimci sako na ba, to kawai ya saurari faya-fayan bidiyo na Bayammen nan mai shiga Binuwai da Filato wato Aleɗ zai ji yadda matashin ke buga kalangu fiye da na Dokta Mamman Shata amma na gagarumin yaƙin basasa a doron addini. Yanzu idan yaƙin ya tashi, masu kamfen ɗin bazata sun ce ƙabila ta fi addini kuma manyan ƙabilu biyu da ke riko da Musulunci wai su raba gari, ko ma su fara fille kawunan juna daga masallatai, rumfunan kasuwanni da sauran magamar jama’a. Ya zama wajibi duk jama’a su riƙa takatsantsan don masu azancin zance sun ce sai wanda ya san inda toka ke tsada ne zai cinnawa rumbunsa wuta. Mu daƙile duk wata kofa da za ta haddasa da na sani.
Ai wargi wuri ya ke yi. In ka ga kare ya na tsalle to a dajin birni ne tare da ‘yan farauta amma ya auka can cikin fadar zaki zai kama kansa. Yara ƙanana da a kan turo su zagi Shehu Mujaddadi su kwana lafiya na yin dabdalarsu a duniyar soshiyal midiya ne don ko ‘yan ƙalilan da kan saka hoto za ka taras an canja ma sa fasali da manhajar AI ko a wanke shi ka ga tunku ya zama gafiya. Masu azancin zance na cewa duk mai cin kasa ya kiyayi ta shuri. Gaggan da kan ingizo yaran nan na can bayan fage sun yi bakam don sun ɗauka asirinsu ba zai tonu ba. Haba ai a duniyar nan dai ta kimiyya da fasaha mu ke.
Don haka ba wata nasara ta ko miskala zarratin da ɓoyayyen mutum ya ke cimmawa wajen ruruta fitina a shafukan yanar gizo. Don wai yara da wasu tarkace sun yi caa su na zagin wani lokaci ɗaya don ya kauce ya barsu su yi rawar banjo, duk ba wani tasirin da ya ke yi fiye da dama a tsakaninsu kuma mun san addini ya raba mu da su. Duk Musulmin kirki ba zai maida rayuwarsa cikin ƙunci da bakar zuciya kamar waɗannan mutane ‘yan gangan ba. Ko masu yin faifan bidiyo da zarar sun fara magana za ka gane makirai ne kawai.
KAMMALAWA
Du wannan rawar jiki da ɗauko sunayen ‘yan siyasa da zagin malamai na musulunci kaɗai da ‘yan bazata ke yi, duk ranar da wani ya yi karambani ya shiga kafar labaru ta gaskiya ya aikata tamkar yadda ya ke yi daga sunkuru zai gane shayi ruwa ne. Ba gagararre sai bararre. Kuma ba dokar da ta ba wa ‘yan gangan lasisin zagin wani. Duk wanda zai fadi ra’yinsa ba cin mutunci kan kowane darasi ya na da dama amma hakan lallai kar ya zama silar cin zarafi ko wulaƙanta wani. Wallahi ba wanda ya hana kowa kafa kungiya ko ma gamayya amma tabbas kar ta zama dandalin kunna fitina da cin zarafin wadanda ya tsana musamman don bambancin addini ko dinka rigar ƙabilanci ta basaja.
Idan kunne ya ji. Don kaunar da na ke yi wa Arewa ta sa na ke jawo hankalin mutanen nan don kar wani ya yi karambani a garin ƙoƙarin miƙa ya yaga mayafinsa ko a yunƙurin wuce inuwarsa ya faɗa rami.
