Zaɓen Shugaba Tinubu: Malamai ban da igiyar zato – Aliyu Salihu Aliyu

Spread the love

Daga HAMISU IBRAHIM a Kano

A tattaunawar da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMISU, ya yi da wani ɗan kasuwa mazaunin Tudun Maliki a Kano mai suna na Aliyu Salihu Aliyu, ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda malamai ke hawa mumbari suna sukar Shugaba Bola Ahmad Tinubu, al’amarin da ya danganta da ƙabilanci da ɓangaranci. A cikin hirar dai ya yi nuni da cewa, wannan ba zai haifar wa Nijeriya ɗa mai ido ba. Don haka ya gargaɗe su kan lallai kada su ɗora mutane a azargagiyar igiyar zato tamkar yadda suka kwata a baya. Ga yadda hirar ta kasance:

Mene ne yake ci maka tuwo a aƙwarya game da malamai da har kake son yin ƙorafi a kansu?

Ina so in ɗan yi wani jan hankali ga malamanmu da suke son yin amfani da addini, wajen cin mutuncin shugabanci na Shugaba Ahmad Bola Tinubu. Shin sun manta ne abin da suka yi ne a baya na Goodluck Jonathan, inda suka rika hawa mumbari suna amfani da addinin Musulunci, suna ci masa mutunci, suna ci wa shugabancinsa mutunci, a kan a kawo namu, ƙabilarmu, yarenmu daya, daga bisani muka zo muka shiga wahala tunda ba mu kawo Allah ba? To ko shi ne, za su ajiye maganar Allah, su kawo kabilanci, suna ta kira ga mutane, kan cewa, wwannan ba kabilarmu ba ne, wai wannan ba zai kara maimaitawa ba, ba zai yi waye, ba zai yi waye ba, kuma har yanzu ba su kawo mana ƙwagwaran dalili ba, ko a ayar ƙur’ani ko a hadisi; kawai suna faɗar ra’ayinsu ne, saboda sun gani bai yi musu abin da suke so ba; ko kuma ba su cimma wata matsaya a cikin bukatunsu da suke tunani ba, shi ya sa suke yi masa hakan. To, mu ba su gaya mana ba. Mu ɗalibansu ne, muna jin su, kuma muna saurarensu. Sai dai a nan ba za mu bi su ba, saboda son zuciyarsu ba. Domin in mun bi su saboda son zuciyar tasu, ba mu ga abin da suka tsinana mana ba.

Alhaji ai suna sukar ne kan matsalar tattalin arziki, wato ga cire tallafin fetur, sannan an ƙaƙaba wa mutane haraji, uwa-uba ga ɗimbin bashi ana ta ciwo wa?

Buhari da ya zo, Gwamnatin PDP nawa ya ce ake binta, alhali shi sai da ya ninka. Shin mene ne ya sanaya basu hau mumbarin sun faɗakar da shi ba, har ta kai ga duk abin da Buhari ya so yi a kasar nan sai ya yi shi, saboda haka aka yi ta shan yunwa ko da za a mutu shi bai fasa ba? Aka zo maganar ture-turen kuɗi ta cikin wayar salula, wato cashless policy,’ har ta kai ga da kuɗinka sai ka zama almajiri. Wai mene ne Buhari ya yi, ba ya waiwayawa baya idan ya yi wani abu; ai gwara Jonathan ma. Domin idan ya yi abu, ya ga jama’a na nuna alamar tunzuri sai ya haƙura , ya ciza, ya ce, to a dawo, saboda ka da a mutu. To, amma mutum nawa ne suka mutu a zamanin Buhari? Idan kuwa maganar ɓarayin daji, masu garkuwa da mutane kake yi, wato Bandits da Kidnappers, a zamanin Buhari mutum nawa aka kashe; an kashe mutane a Zamfara, an kashe mutane a Sakkwato. Kai a ina ne ba a kashe mutane ba? Kai akwai lokacin da aka yi wasu kashe-kashe a Zamfara, Buhari ko kula mutane bai yi ba, sai kawai ya tafi Legas wajen binne wani hamshaƙi. Yanzu shi ne, Tinubu, don ya je Jos, inda ya je ya jajanta, sai ake ta surutu a kai. Ai musulmi da Kirista aka kashe, ya tafi ya jajanta musu.

Ba wai goyon bayan Gwamnati kadai ba, shin wacce shawara za ka bayar domin samun mafita?

Ai mafita tana nan tare da mu cikin yardar Allah, domin shugabannin harkar tsaron ƴan Arewa Shugaba Bola ahmad Tinubu ya fara naɗawa, wato Muhammadu Badaru, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, tare da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Matawalle. Idan kuwa haka ne, to mene ne zai hana Malamai su gana da su, a tattauna a yi aiki tuƙuru har a lalubo bakin zare. Amma saɓanin haka sai ƙoƙari suke su zarga mana igiyar zato don ganin ba a zaɓi Shugaba Bola Ahmad Tinubu ba. 

To idan ma ka ƙi zaɓensa, wane ne aka kawo mafi nagarta da muke da tabbaci zai yi wa al’ummar ƙasar nan abin da ya dace a tsarin tattalin arziki da zamantakewa da siyasa?

Gaskiya bai dace ba, a cewarsa wai malamai su hau mumbari suna sukar shugaba saboda kabilanci da ɓangaranci.

Su tuna shi fa Musulmi ne. wai ko so suke yi ya zo gabansu ya sake yin wata sabuwar kalmar shahada?

Ina roƙon malamai su fito su bayyana mana abin da suke nufi. Domin ni ɗan kasuwa, kuma babu wani da zai ce na karɓi kwandalarsa. Saboda haka na fi goyon bayan Bola Ahmad Tinubu. Kuma ina ganin akwai bukatar mutane lallai su fahimci gaskiyar lamari, kan cewa, kowane shugaba yana da gwazonsa na aiki, akwai kuma naƙasunsa. Bisa la’akari da wadannan al’amura nike ganin ya dace a daina tada jijiyar wuya kan lallai sai an hana Tinubu ya sake yin takarar zabe, har ya ƙarasa wa’adin mulkinsa zango na biyu. Ko ba komai, idan har malamanmu suka gana da shi, suna da alfarma bayar da shawarwari kan yadda za a gudanar harkokin mulkin ƙasar nan. Uwa-uba, za a iya samar da mafita daga matsalar tattalin arziki da tsaro, har ma da hargitsin siyasa. Don haka ina ƙara yin kira da babbar murya, matuƙar malamanmu sun yarda da gaskiya, to sai mu hada ƙarfi da Gwamnati don tsamo ƙasar nan daga ruɗani. Ina ganin suna da martabar da har yanzu Shugaba Bola Ahmad Tinubu zai saurare su, ya kuma yi aiki da irin shawarwarinsu, wadanda maɓuɓɓuga ce daga littafan addini, wadanda babu son rai a ciki, kuma ba su karo da dokokin ƙasa ba; hasali ma sai dai a ce inganta  za su yi.

By ukarofi