‘Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin Ganduje, ‘yan sanda uku sun jikkata

Daga IBRAHIM HAMISU

‘Yan bindiga sun kai wa tawagar motocin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, hari ran Talata da daddare a kan hanyarsu ta komawa Kano daga Zamfara.


Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa harin ya yi sanadiyar jikkata wasu ‘yan sanda uku daga tawagar.

Bayanai sun nuna yayin harin, Gwamna Ganduje na cikin motar gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru tare da shi.

Majiyar Manjaha ta bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ke cikin tawagar da kuma ‘yan bindigar inda wasu ‘yan sanda uku suka ji rauni sakamakon harbin bindiga.