‘Yan bindiga sun kashe mutane 16 a ƙauyen Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane 16 a wani mummunan hari da suka kai a ƙauyen Kiliya da ke a garin Bagagadi a ƙaramar hukumar Dutsinma.

Harin da yabar wasu da dama ɗauke da raunuka ya faru ranar juma’a a lokacin da mutanen ƙauyen ke cigaba da bukuuwan sallah.

Kamar yadda wasu mutanen ƙauyen da suka nemi a ɓoye sunan su,sun faɗa cewa ‘yan bindigan sun fara shigowa ƙauyen a kan babura guda biyu da ganin haka mutanen ƙauyen suka fara gujewa ƙauyen.

Sai dai majiyar mu ta shaida cewa nan take ‘yan bindigan suka hana mutanen garin barin ƙauyen,sai da ‘yan bindigan suna ƙara shigowa ƙauyen a kan babura da dama suka shiga harbe harbe a ƙauyen.

Kamar yadda bayanai suka nuna sama da mutum 400 suke neman mafaka a garin Bagagadi wasu kuma sun tsallaka zuwa garin Raɗɗa neman ɗauki,”wasu kuma da dama ‘an bindigan suka hallaka a gonakin su.

Wani yaro ɗan shekara 14 mazaunin ƙauyen kiliya ya shaida cewa shi da idon sa yaga babura guda biyu ɗauke da ‘yan bindaga daga baya yaga ƙarin shigowan su ɗauke da muggan makamai “nan take suka fara harbe harbe kan mai uwa da wabi a ƙauyen.

Wani ɗan asaline ƙauyen Bagagadi ya ce yanzu haka akwai mutanen fiye da 30 daga ƙauyen Kiliya,waɗanda yawancin su ƙananan yara da mata sun sami mafaka a garin Bagagadi.

Koda aka tuntuɓi jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘an sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa har yanzu basu sami wani rahoton afkuwar lamarin ba sai dai ya ce da zaran bayanin ya shigo masu zai tuntuɓi manema labarai.

By ukarofi

Leave a Reply