’Yan bindiga sun kashe mutane 21 a Jihar Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mutane 21 a Baton da Rayogot da ke gundumar Heipang a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.

Rwang Tengwong, sakataren yaxa labarai na Ƙungiyar Berom Youth Movement, BYM, wata ƙungiyar al’adu da zamantakewa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Jos.

Mista Tengwong ya ce harin da aka kai kan al’umomin ya faru ne da ƙarfe 1:26 na safiyar ranar Alhamis, kuma ya yi sanadin jikkata wasu mutane bakwai.

Tengwong, wanda ya yi tir da hare-haren ba gaira ba dalili a wasu sassan jihar, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen ganin an kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a jihar.

“Mutane 21 ne aka kashe a wani hari da aka kai a wasu ƙauyuka biyu a gundumar Heipang da ke Barkin Ladi.

“Maharan, waɗanda suka zo da misalin ƙarfe 1:26 na rana sun kashe mutane 17 a Batin na garin Heipang yayin da aka kashe wasu huɗu a Rayogot.

“Wasu mutane bakwai sun samu raunuka daban-daban,” inji shi.

Kakakin, ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da su kwantar da hankalinsu kuma su kasance masu bin doka da oda.

A martanin da ya mayar kan lamarin, Gwamna Caleb Mutfwang na Filato ya yi Allah-wadai da hare-haren tare da yin kira ga jami’an tsaro da su zaqulo waɗanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Allah wadai da matakin da Mista Mutfwang ya yi ga hukumomin tsaro na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Gyang Bere, Daraktan Ya a Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan, Doppa ya fitar a Jos.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *