‘Yan bindiga sun sace mutum 33 a Kachia, har da mace mai ciki

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna aƙalla mutum guda ya mutu sannan an sace mutum 33 sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin ƙaramar hukumar Kachia da ke jihar.

Harin wanda ya auku a Larabar da ta gabata da daddare a cikin Kachia, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

Dakacin gundumar Kachia, Malam Idris Suleiman ya tabbatar da aukuwar harin a lokacin da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, tare da jami’an tsaro suka ziyarci yankin.

Suleiman ya ce ‘yan bindigar sun zo ne da yawansu da misalin ƙarfe tara na dare sannan suka soma harbe-harben bindiga don saka tsoro da kuma firgitar da mazauna yankin.

Ya ce ɓarayin sun soma da wani gidan biredi ne inda suka ɗauki mutum 5 tare da kashe direban mai gidan biredin kafin daga bisani suka koma yankin Mother Cat inda a nan suka kwashi mutum 28, ciki har da wata mace mai ciki.

Ya ci gaba da cewa, ɓarayin sun shiga shaguna da dama sun kwashi kayayyaki masu yawan gaske bayan da masu shagunan suka tsere don tsira da rayuwarsu.

A lokutan baya-bayan nan dai jihar Kaduna ta rasa sukuni saboda addabar da ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji suka yi mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *