Juma’a Buhari zai tafi Landon a bisa dalilin duba lafiyarsa

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai koma Landon ranar Juma’a kan batun da ya shafi kula da lafiyarsa.

Sanarwar da mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Femi Adesina, ya fitar ta nuna bayan tafiyar, Buhari zai dawo gida Nijeriya ne a mako na biyu na watan gobe.

Adesina ya ce,  “Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landon ran Juma’a, 25 ga Yuni, 2021 bisa dalili na duba lafiyarsa.

“Sannan ya dawo a mako na biyu na Yuli, 2021″.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *