‘Yan bindiga sun saki mai yi wa ƙasa hidima bayan biya Naira miliyan biyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindiga sun saki ‘yar yi wa ƙasa hidima (NYSC) da suka sace a Kaduna, bayan sun cika sharuɗan da suka gindaya masu na biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu da katin waya na Naira dubu 100 da kuma babur.

Faith Onoriode, wacce ta kammala Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Otefe, Oghara da ke Jihar Delta, a Tsangayar Nazarin Halittu da Ilimin Kananan Halittu (Biology/Microbiology), an sake ta ne bayan an cimma matsaya tsakanin iyayenta da waɗanda suka sace ta.

SaharaReporters ta ba da rahoton cewa, Onoriode, an sace ta ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da ta nufi sansanin ‘yan yi wa ƙasa hidima da ke Jihar Jigawa ranar 21 ga Maris, 2022.

Bayan an sallame ta dai, tuni aka garzaya da ita asibiti domin a duba lafiyarta.

Kamar yadda ɗaya daya cikin ‘yan’uwan Onoriode ya bayyana wa majiyar tamu, ‘yan bindigar da suka sace ta sun buƙaci a kawo masu mashin da wayar salula ƙirar Tecno guda biyar da katin waya da Naira miliyan biyu.

Festus Onoriode ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar sun faɗa masu irin kalar mashinan din da suke buƙata da wayar salular da katin wayar da suke so. Sun tura masu katin waya Naira dubu 100 da kuma kudi Naira miliyan biyu.

“Mun biya Naira miliyan biyu da katin waya na Naira dubu 100. Dama sun nemi wayar salula ƙirar Tecno ce guda biyar. Irin mashin din da suke so, kuma ba a samun sa a Kaduna, sai a Legas.

“Bayan mun shirya, mun cika duk sharuɗɗan da suka gindaya mana, sai muka kira muka faɗa masu. Sai suka ce mu samu ‘yan rakiya da za su raka mu wajensu. Su kuma ‘yan rakiyar waɗanda suka haɗa da. Sojoji guda 10, sai suka ce sai mun biya su Naira dubu 300 a matsayin ladan rakiya.

“Da yake sojoji ne guda 10 suka raka mu. Ko da mun je wajen duba ababen hawa, ba mu samu matsala ake barinmu muna wucewa. Mun je mun jira su. Daga bisani aka fito da ita da misalin ƙarfe 6 zuwa 7 a ranar Lahadi. Kar Allah ya maimaita mana wannan masifar.

“Tana Asibiti yanzu tana amsar magani. Muna godiya ga jami’an tsaro a kan irin gudummawar da suke ba mu. Haɗa kuɗin fansar nan ba sauƙi. Mun gode wa Allah da ta fita,” inji Festus Onoriode.