Daga UMAR GARBA a Katsina
Wasu gungun mutane ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun sace mutane 13 a garin Natsinta da bai wuce nisan kilomita 5 ba tsakanin sa da babban birnin Jihar Katsina.
’Yan bindigar waɗanda suka yi ɓadda sahu don kuwa sun ajiye baburan su a kusa da wani ƙauye dake maƙotaka da garin na Natsinta inda suka ƙaraso a ƙafa zuwa garin da su ka yi ta’addancin.
Wani Hamisu Ahmad da harin ya rutsa da ƙanwarsa ya shaida wa Manhaja cewar ‘yan bindigar sun shigo garin da misalin ƙarfe 10:00 na daren Laraba.
Wata da harin ya rutsa da ita kuma muka sakaya sunanta ta bayyana cewar ‘yan bindigar sun riƙa shiga gida gida suna ɗibar mutanen garin.
Ta kuma bayyana cewa, ‘yan ta’addar sun bi su har cikin gidajen su tare da yi ma su barazar idan ba su ba su haɗin kai ba za su hallaka su hakan ya sa su ka amince su ka bi ‘yan bindigar zuwa daji.
Ta ci gaba da cewa, duk da tana cike da fargaba amma za ta iya tuna yadda ‘yan bindigar su ka kora mutane kamar dabbobi su fiye da ashirin waɗanda suka haɗa maza, mata da ma ƙananan yara.
Sai dai daga bisani wasu mutane kimanin 13 sun samu kuɓutowa daga hannun ‘yan ta’addar dab da wayewar garin yau Alhamis.
Bayanai sun tabbatar da cewa yanzu haka dai ‘yan bindigar sun tafi da mutane aƙalla 13 waɗanda su ka haɗa maza da mata da kuma ƙananan yara.
Duk da kasancewar barikin rundunar sojin Nijeriya da ke Katsina tana cikin garin na Natsinta hakan bai hana ’yan ta’addar kutsawa ba don gudanar da aikin ta’addanci.