Matsalar tsaro: Sufeto Janar ya bada umarnin tattara bayanan babura

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

A cikin fargabar taɓarɓarewar tsaro a sassan Nijeriya da ke haifar da kashe-kashe da raunata ’yan ƙasa a kowace rana, Sufeto Janar na ’yan sanda Nijeriya, Usman Alkali Baba ya umarci mataimakin sufeto Janar na ’yan sanda na shiyoyin ’yan sandan Nijeriya da kwamishinonin ’yan sanda na jihohin ƙasar nan da su fara tattara bayanan duk wani babura da masu tuƙa babur mai ƙafa uku da ke yankunansu domin tsaron lafiyar ’yan ƙasa.

Alkali ya kuma amince da gudanar da wani muhimmin taron ƙara wa juna sani kan harkokin tsaro na ɗaukacin sassan AIGs, APs da sauran kwamandojin rundunonin tsaro na rundunar a shiyyoyi shida na ƙasar da kuma babban birnin ƙasar nan domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.

Ya ba da wannan umarni ne a ranar Laraba a taron da IGP ya yi da kwamandojin ’yan sanda masu dabaru a hedikwatar runduna da ke Abuja, ranar Laraba, inda ya yi Allah wadai da yawaitar barazanar tsaro ga ‘, yan ƙasa da masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ke yi.

A cewar shugaban ’yan sandan, duk da matakan tsaro da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro su ka ɗauka, irin yadda waɗannan ƙungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi ke kai wa ga ‘yan ƙasa hare-hare yana ƙara ta’azzara ne sakamakon ƙaruwar safarar makamai da yaɗuwarsu.

Ya ƙara da cewa, lamarin ya ƙara taɓarɓare harkokin tsaro a ƙasar, kuma a baya-bayan nan ne aka kai hari a gidan gyaran hali da ke Kuje inda wasu manyan masu aikata laifuka suka tsere.

A cewar IGP ɗin, yayin da ’yan sanda tare da sauran jami’an tsaro suka yi nasarar sake cafke wasu daga cikin masu laifin da suka gudu tare da inganta tsaron wurin, lamarin da kuma ƙaruwar ta’addancin da ƙungiyoyi masu xauke da makamai ke yi a ƙasar ya haifar da hakan zuwa ga fargaba a tsakanin ‘yan ƙasa da kuma ci gaba da gabatar da babbar barazana ga tsaron ƙasarmu.

Taron ya kuma yi nazari kan iyakar bin umarninsa da hukumomin ‘yan sanda ke hulɗa da hukumomin gyaran halin na Nijeriya a sassan da suka rataya a wuyansu tare da yin nazari tare da duba ayyukan tsaro da ake da su domin gano matsalolin da ke cikin wuraren da ake tsare da su tare da ba da taimako wajen inganta tsaro a ciki da kuma kewayen irin waɗannan wurare don hana ci gaba da taɓarɓarewar tsaro.

A halin da ake ciki, yayin da zaɓukan shekarar 2023 ke ƙara gabatowa a kowace rana a Nijeriya, IGP ya amince da wani muhimmin taron ƙara wa juna sani na tsaro da za a gudanar domin inganta ayyukan gudanar da harkokin tsaro a ƙasar.

Bugu da ƙari, za ta gudanar da shiyyoyi shida na ƙasar da nufin horar da jami’an ’yan sanda kusan ɗari huxu tare da guraben aikin da aka ware wa sojoji, da ma’aikatar harkokin gwamnati da sauran jami’an tsaro waɗanda ke taimaka wa rundunar ’yan sandan Nijeriya wajen gudanar da harkokin tsaro a zaɓe.

IGP ya ce, shirin an yi shi ne musamman domin ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan jami’an tsaro kan harkokin tsaro da kuma samar da ƙwararrun hanyoyin sadarwa da za a iya amfani da su domin sauya labaran yadda ake gudanar da zaɓe a lokacin babban zaɓen 2023.