Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa a mako mai zuwa ne za a soma sanya kayan aiki ga asibitin koyarwa ta Jami’ar jihar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato Dr. Ali Mohammad Inname ne ya sanar da haka a yayin gudanar da wani taro da wakilan kamfanin da aka bai wa aikin Thomat Company Nigeria Ltd, taron da ya gudana a harabar asibitin.
Dr. Muhammad Ali Inname, ya ce wannan ya biyo bayan amincewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na cefano kayakin tare da sanya su, kuɗin da suka kai kimanin Naira Biliyan 12.
A cewarsa, za a gudanar da aikin ne rukuni-rukuni, kasancewar aikin yana da yawa.
Dr. Inname ya jaddada cewa za a soma sanya kayan aikin ne a sashen kulawa da mata da ƙananan yara, da kuma ɗakunan masu gata wato Amenity, da sauran muhimman wurare.
Kwamishinan haka ma ya bayyana fatan da yake da shi na ganin asibitin ta soma aiki farkon watan Janairun baɗi.
Daga ƙarshe ya umurci kamfanin da aka bai wa kwangilar aikin da ya hanzarta kammala aikin cikin lokaci.
Wannan na ƙunshe ne cikin wani bayani mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jiha Nura Bello Maikwanci.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato Dr. Ali Mohammad Inname ne ya sanar da haka a yayin gudanar da wani taro da wakilan kamfanin da aka bai wa aikin Thomat Company Nigeria Ltd, taron da ya gudana a harabar asibitin.
Dr. Muhammad Ali Inname, ya ce wannan ya biyo bayan amincewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na cefano kayakin tare da sanya su, kuɗin da suka kai kimanin Naira Biliyan 12.
A cewarsa, za a gudanar da aikin ne rukuni-rukuni, kasancewar aikin yana da yawa.
Dr. Inname ya jaddada cewa za a soma sanya kayan aikin ne a sashen kulawa da mata da qananan yara, da kuma ɗakunan masu gata wato Amenity, da sauran muhimman wurare.