Ya kamata gwamnati ta ƙara wa’adin rajistar zaɓe, cewar ’Yar takarar kansila a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

An bayyana buƙatar da ke akwai ga Gwamnatin Tarayya da ta duba yuwar ƙara wa’adin ci gaba da rajistar masu zaɓe, da hukumar INEC ta dakatar.

Wata ‘yar takarar kansila a mazaɓar Sanyinnan dake Ƙaramar Hukumar mulkin Tanmbuwal Hajiya Daraja Shehu Sanyinnan ce ta yi wannan kiran cikin wani bayani da ta fitar.

Ta bayyana cewa ƙara lokacin rajistar masu zaɓen zai bayar da dama ga waɗanda suka kai munzalin jefa ƙuri’a yankar rijistar domin su samu damar jefa ƙuri’a a babban zaɓen gamagari da ke tafe.

Haka ma Daraha Shehu ya yaba wa matar ɗan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato na Jam’iyyar PDP Hajiya Hindatu Sa’idu Uma Ubandoma akan yanda ta duƙufa ka’in da na’in wurin neman goyon bayan jama’a musamman mata abinda ta ce yunƙurin na samun karvuwa.

Da ya juya akan ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP kuwa, bayyana shi a matsayin nagartaccen mutum wanda ka ‘iya kai wannan jiha ga tudun muntsira muddin aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jiha a baɗi in Maiduka Ya kai mu.

Ta bayyana cewa la’akari da irin kyakkywan tarihin da Sa’idu ya kafa a sa’ilin da yake ma’aikacin banki, da kuma kasancewar mamba a majalisar zartaswa ta jiha, ba a taɓa samun shi da aikata rashin gaskiya ba.

Daga ƙarshe Daraja Shehu ta bayyana cewa Sakkwatawa na mararrin Ubandoma ya mulke su saboda suna kyautata masa zaton zai kawo gagarumin ci gaba, wajen inganta rayuwar matasa mata da maza, yara da dattawa.