‘Yan fashi sun babbake gomman matafiya a Sakkwato

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga jihar Sakkwato sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ake yi zargin ‘yan fashin daji ne sun ƙona wasu matafiya a kan hanyarsu bayan da suka taso daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni.

MANHAJA ta kalato cewa, mummunan al’amrin ya auku ne da misalin ƙarfe tara na safiyar jiya Talata a kusa da ƙauyen Gidan Bawa, wurin da aka ce ‘yan fashin sun saba tare matafiya tare da ƙona abubuwan hawa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa kimanin mutum 17 suka mutu a harin.

Ya ce motar da lamarin ya shafa na ɗauke ne da fasinjoji 24 ne wanda daga cikin wannan adadi mutum 7 na wani asibitin da ba a bayyana sunansa ba suna jinya, yayin da sauran sun ƙone ta yadda ba za a iya gane su ba.

Sai dai wasu majiya daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni sun yi iƙirarin cewa adadin waɗanda ke cikin motar da aka ƙona ya zarce abin da ‘yan sanda suka bayyana. Domin akwai dangin da ya rasa mutum 10 a ibtila’in.

Majiyar jaridar Leadership ta ce, lamarin abu ne da ya taɓa zuciya matuƙa, tare da cewa suna ci gaba da ƙoƙarin tantance adadin mutanen da harin ya rutsa da su wanda ka iya zama abin tsoro ainun.