Babu tabbacin rigakafinmu ya yi tasiri kan nau’in Omicron – Moderna

Kamfanin Moderna da ke jerin kamfanonin da ke aikin samar da rigakafin Korona ya ce, ba shi da tabbacin nau’in rigakafinsa ya iya tasiri kan sabon nau’in cutar na Omicron da ke ci gaba da zama barazana bayan yaɗuwarsa a ƙasashe da dama.

Kamfanin Moderna na Amurka ya yi gargaɗin cewa sabon nau’in covid-19 na Omicron na da saurin yaɗuwa fiye da hasashe duk da cewa kawo yanzu babu rahoto kan wanda ya kashe.

Stephane Bancel shugabar kamfanin na Moderna a wata zantawarta da ‘Financial Times’ ta ce, nan da makwanni biyu ake sa ran kammala tattara bayanai game da zubi ko kuma yanayin nau’in na Omicron, sai dai saurin yaɗuwarta bayan vulla a Turai da kudancin Amurka cikin ƙasa da mako guda bayan bayyanarta a Afrika ta kudu abin fargaba ne matuƙa.

A cewar Stephane duk zantawarta da masana kimiyya game da sabon nau’in na Omicron su kan bayyana mata matuƙar fargabarsu kan illar da nau’in ka iya yi.

Hasashen masana dai na ganin mai yiwuwa sabon nau’in na Omicron ya iya bijirewa nau’ikan rigakafin da ake da su yanzu, musamman bayan da Moderna da kansa ya ɗiga ayar tambayar cewa babu tabbacin nau’in rigakafinsa ya iya tasirin yaƙar Omicron.

Tuni dai qasashen duniya suka tsaurara matakai ciki har da waɗanda suka fara kulle iyakoki duk dai a yunƙurin daƙile yaɗuwar nau’in na Omicron da aka samu ɓullarsa makon jiya a Afrika ta kudu.

Yanzu haka dai kamfanonin da ke aikin samar da rigakafin da suka ƙunshi Moderna na Amurka da haɗakar Pfizer da BioNTech da kuma Sputnik V na Rasha dukkaninsu sun sanar da nisa a bincike kan nau’in na Omicron don samar da kariya.

Moderna ya bayyana cewa da yiwuwar nau’in Omicron ya ɗara na Delta a haɗari tare da zama babbar barazana ga ƙasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *