‘Yan Nijeriya na ci gaba da alhinin mutuwar jarumi Emmanuel France 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitaccen jarumi da ya ga jiya da yau, wanda ya jima yana ƙawata akwatun talabijin ɗin masu kallo da irin baiwar da Allah Ya ba shi, Emmanuel France ya mutu yana da shekaru 80. Saidai har zuwa yanzu da jama’a ke jimamin rabuwa da jarumin, ba a samu wani ƙwaƙwaran bayani kan abinda ya yi sanadin mutuwar tasa ba. Sai dai abinda kawai aka sani, fitaccen mai shirya finafinai Femi Ogedengbe, wanda ya yi ayyuka da dama tare da marigayin ne ya tabbatar da nutuwar shi, bayan ɗan lokaci ana raɗe-raɗin mutuwar tasa.

Jarumi Emmanuel France, ɗan asalin ƙasar Ghana ne, kuma jajirtacce da ke da sha’awa da baiwar iya yin fim. Burinshi da kuma sha’awar harkar fim ta kai shi ga zama jarumi a babban fim ɗin nan mai suna ‘Ghana Must Go’.

Matuƙa ya bayar da gudunmawa a masana’antar Nollywood, don haka mutuwar tasa ta zama rashin wani giɓi a masana’antar.

By ukarofi