‘Yan Nijeriya za su fara hada-hadar E- Naira a wayar salula nan da mako mai zuwa – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, nan da mako mai zuwa ‘yan Nijeriya za su iya hada-hadar kuɗin ta lalitar E-Naira a wayoyin hannunsu nan da mako mai kamawa.

Shi dai tsarin E-Naira tsari halstacce a doka na amfani da fasahar zamani wajen hada-hadar kuɗin a yanar gizo.

Bayan hada-hadar kuma, gwamnan CBN ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya za su iya buɗe lalaitr E-Naira a wayoyinsu na hannu.

A cewarsa, kawai za a danna *997# a cikin wayar hannu domin yin hada-hadar E- Naira a wayoyin hannu.

Kuma kowa zai iya amfani da shirin. Daga masu ajiyar a banki da waɗanda ba su da asusun bankin. Hakan zai ba wa kowa damar iya hada-hadar kuɗi ta hanyar fasahar zamani, inji shi .

Emefiele ya yi wannan jawabin ne a yayin taron ƙaddamar da E-Naira ranar Litinin a Abuja.