‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta ce ta samu nasarar daƙile sace mutane a wasu sassan jihar.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya shaidawa manema labarai haka. Ya kuma tabbatar da ceto mutum shida da ‘yan sandan su kayi.
Ya ce ɗaya lamarin ya faru ne a hanyar kauran Namoda zuwa Katsina a cikin dare bayan ‘yan sanda da haɗin gwiwa na sojoji sukai bata kashi da ‘yan bindigan.
Sakamakon arangama da jami’an tsaro su ka yi da ‘yan bindigan inji ASP Sadiq, sun sami ceto mutum huɗu,
sai dai ɗaya daga cikin waɗanda aka ceton ya sami raunuka bayan harbin sa da ‘yan bindiga su ka yi.
Dukan su dai su suna babban asibiti a Katsina,da zarar an gama duba lafiyar su za a miƙa su ga iyalan su.
Haka kuma mai magana da yawun ‘yan sandan yace wani yunƙuri da ‘yan bindiga su ka yi na sace wasu mutane a unguwar Boka akan hanyar faskari zuwa Gusau bai sami nasara ba.
ASP Sadiq yace, jami’an tsaro sun sami nasarar kuɓutar da mutum biyu a yayin da wani ya rasa ransa.
Ya yabawa al’ummar waɗannan yankuna. da irin haɗin kai da suke baiwa jami’an tsaro ta hanyar bada bayanai cikin gaggawa na ɓullar ‘yan bindiga a yankunan su.
