Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Zimbabwe ta amince da yanke giwaye 200 don ciyar da ’yan ƙasar da ke fama da yunwa.
Mai magana da yawun hukumar kula da wuraren shaƙatawa da namun daji na Zimbabwe, Tinashe Farawo, ya tabbatar wa CNN da faruwar lamarin a ranar Litinin.
“Muna nufin yanka giwaye 200,” inji Farawo, yayin da yake koka da yadda ake samun ƙaruwar rikicin giwaye da ‘yan adam a sanadiyyar rashin isasshen abinci da ake fama da shi sakamakon tsananin fari a ƙasar da ke gabashin Afirka.
Ya ƙara da cewa, “Dabbobin suna yin ɓarna sosai a cikin al’umma, suna kashe mutane. A makon da ya gabata mun rasa wata mata a yankin arewacin ƙasar da giwa ta tattaka ta.
“A makon da ya gabata ma haka lamarin ya faru. Don haka giwaye sun zama masu kisan kai, yanka su itace kaɗai mafita”.
A cewar kafafen yaɗa labarai na cikin gida, a bana, sama da mutane 30 ne aka kashe a rikicin namun daji da ’yan adam a Zimbabwe.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Farawo ya ce matakin na kuma daga cikin ƙoƙarin da ƙasar ke yi na rage cunkoso a wuraren shaƙatawa na ƙasar, waɗanda ke iya ɗaukar giwaye 55,000 kawai. ƙasar Zimbabwe tana da giwaye sama da 84,000.
Majalisar ɗinkin Duniya ta yi kiyasin cewa sama da mutum miliyan bakwai na fuskantar barazanar yunwa a Zimbabwe, inda ta ayyana ƙasar da ke gabashin Afirka “a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da ake fama da yunwa.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar a farkon watan Agusta, MDD ta ce, Wani sabon rahoto daga ofishin kula da ayyukan agaji na MDD (OCHA) ya nuna cewa matsalar ƙarancin abinci a ƙasar Zimbabwe na ƙara taɓarɓarewa cikin sauri bayan da aka yi ta fama da fari a sakamakon yanayin ‘El Nino’.
Shirin kashe giwaye na Zimbabwe ya zo ne makonni bayan da gwamnatin Namibiya ta ɗauki wannan mataki na magance matsalar ƙarancin abinci da kuma rikicin namun daji da na bil’adama yayin da fari ke ƙara ƙamari.
