Darussan labarin Hussaina, matar Seaman Abbas

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

1. Taura biyu ba ta tauno: Tsarin aikin soja a Nijeriya ƙarƙashin tsarin mulki mara addini ya ke ‘secular’, don haka duk wanda ya ɗauki rantsuwar aikin, ya san dokar soja na da fifiko a kan ta addini. Da Abbas da mai gidansa duk Musulmi ne, amma Colonel Muhammad ya yarda cewa dokar soja ta fi ta addini ƙarfi. Don haka ya yi ƙoƙarin ladabtar da Abbas wanda ya bar wajen aikinsa, domin yin sallah.

2. Girmama na gaba: A duk tsarukan rayuwa, walau na addini ko akasin haka, biyayya wajibi ce. Abbas ya kamata ya saurari raddin shugabansa, ba ya yi sa-in-sa da shi ba. Wanda hakan ya tunzura lamarin.

3. Fushi na kawo da-na-sani: Fushin da Abbas ya yi, saboda tunanin cewa, sallah fa ya je ya yi, don me za a yi masa wannan tuhuma, ya sa shi bijire wa shugabansa, ta hanyar ƙin miƙa makaminsa, wanda har kunamar bindiga ta ƙwace. Wannan babban laifi ne a aikin soja (insurbodination). Dalilin da ya sa a ka yi masa zalunci na tsawon shekaru shida.

4. Rashin adalci ba shi da kyau: Laifin Abbas ko kusa bai cancanci irin wannan azabtarwa da hukumomin soja su ka yi wa wannan bawan Allah ba. An tsare shi a gadirun, babu shari’a tsawon shekaru shida yadda har abin ya taɓa ƙwaƙwalwarsa, hakan tsabar rashin Imani ne.

5. Mace ta gari: Duk cikin ni’imomin duniya babu abinda ya kai mace ta gari. Hussaina mace ce ta gari, domin ta nuna ƙauna, jimuri, jajircewa da amana a kan mijinta, duk da rashin gata ko tallafi, sai da ta sanar da duniya halin da mijinta ke ciki da irin zaluncin da aka yi masa. Allah ya saka mata da aljanna.

6. ƙarfin kafar sadarwa: Cikin awa 24 da bayyanarta a shirin Berkete Family, ’yan Nijeriya kusan miliyan biyu sun kalli bidiyonta da aka yaɗa a ‘social media’ yadda miliyoyi sun faɗi albarkacin bakinsu, manyan ƙungiyoyi irinsu ‘Northern Elders Forum’ sun sa baki har rundunar soja ta fitar da bayani. Zaluncin shekara shida ya ja burki cikin awa 24.

7. Jinjina ga aikin jarida: Aiki ne kamar kowanne, wanda zai iya kai mutum wuta ko aljanna. Idan ka tsare gaskiya a aikin kamar yadda Shugaban Talabijin na Berkete, The Ordinary President, ya yi shekaru ya na yi, ta hanyar maida hankali wajen yaƙar zalunci, insha Allah wannan lamari zai ba shi damar samun ceto a lahira. Haka nan waɗanda ke amfani da aikin domin biyan gajeriyar buƙatarsu, ta hanyar karewa ko yaɗa ƙarya, su saurari haɗuwa da Ubangiji. Allah ya ƙara ɗaukaka Berkete Family Tɓ.

8. Mugwaye na nan a laɓe: Saboda ginuwar aikata cuta ta hanyar damfara (sakamakon rashin aiki da tarbiyya) wasu kullum na ƙoƙarin gina kansu a kan cutuwar wasu. A wannan lamarin na Hussaina, har wasu sun bazamo da zancen yi mata gidauniya. Alhamdulillah, Ordinary President na Berkete Family ya yi maza ya sanar da cewa, idan za a yi mata gidauniya, za ta fito Berkete ta faɗa kuma ta bayar da asusunta na banki.

Idan muka duba waɗannan abubuwa, ya kamata shugabanni su gane cewa, zalunci ba ya ɗorewa, domin komai daren daɗewa, wata rana Allah zai karya wannan zalunci. Hukuncin da aka yi wa Seaman Abbas ya wuce hankali. Kuma muna gani ana yaɗa bidiyoyi na ’yan ta’adda waɗanda su ke amsa laifin kashe mutane barkatai, amma ba a yanke musu hukunci cikin gaggawa ba. ɓarayin daji da na cikin gari masu sata da biro na yawo babu tsangwama. Wajibi a yi bincike kan lamarin Abbas kuma a biya shi da iyalansa diyyar zaluntar sa da aka yi na tsawon waɗannan shekaru kuma a hukunta masu hannu a ciki.

Sannan ’yan Arewa mu farka mu gane cewa, akwai babban makami a hannunmu guda biyu waɗanda za su iya magance mana yawancin matsalolinmu. Wato amfani da ƙarfin sahar sadarwa da kuma haɗe baki wajen yaƙar zalunci. Wannan labari na Hussaina shi kaɗai ya nuna mana yadda ƙarfin amfani da ‘media’, don tursasa canji. ’Yan shekarun baya a lokacin Buhari, mun tuna wata yarinya da aka yanke wa hukuncin kisa a Saudiya bisa tuhumar safarar ƙwaya a bisa kuskure. Amma da muka yunƙuro ta hanyar ‘social media’, sai da aka tursasa Buhari ya saka baki, inda ya yi magana da Shugaban Saudiya kuma aka yi nasarar ceto ranta. ƙarfin da muke da shi kenan, amma muke sakaci da shi.

Nijeriya a yau, mu ne na biyu a duniya bayan Philippines, wajen amfani da ‘social media’, kuma binciken ‘American Embassy’ a Nijeriya ya nuna cewa, Jihar Kano ce ta ɗaya a amfani da ‘social media’ a ƙasar. Don me za mu riƙa ɓata kuɗaɗenmu wajen kallon sakarci da shirme, tare da azurta masu sakarcin da shirmen alhali mu na iya yin irin wannan aiki na Hussaina, domin kawo canji a al’ummarmu?

Idan muka haɗu waje guda babu wanda zai iya laƙuce mana hanci. Kwanan nan mun ga yadda shugaban ƙasa, ECOWAS, Amurka da ƙawayenta su ka so jefa mu yaƙi da ’yan uwanmu na Sahel (Nijar, Mali da Barkina Faso), amma ’yan Arewa (malamai, ’yan boko, attajirai, mawadata, sarakuna da talakawa) su ka ce “mun ƙi’ dole aka haƙura aka bi hanyar laluma.

Yadda aka haɗa kai wajen Allah wadai da zaluncin da ake yi wa Abbas, na tabbata zai kawo wa iyalin ƙarshen wannan masifa.

Mu sani cewa an kassara Arewa kuma daf mu ke da durƙushewa, amma matuƙar za mu ci gaba da amfani da waɗannan makamai guda biyu, ƙarfin ‘social media’ da haɗin kai wajen tunkarar matsalolinmu, kamar sa ido ga ’yan siyasa da alƙalai da sauran ma’aikata, wallahi babu wanda ya fi ƙarfinmu. Kuma da lallai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci muna iya kawo ƙarshen matsalolin tattalin arziki, cin hanci da tsaro waɗanda su ka addabi Arewa a yau.

Allah ya farkar da mu ya kuma agaza mana.

Ali Sadiƙ mai sharhi kan harkokin yau da kullum kuma mazaunin Kano. Sannan za a iya samun sa a wannan lambar waya 08039702951

By ukarofi