Daga HASSAN IMRAN
Assalamu alaikum. ’Yan uwana, yau na zo da wata taƙaitacciyar nasiha ne akan matsalar garkuwa a ƙasar nan, da nufin ba da shawarwari da samar da mafita.
Daga cikin matsalolin da suka adabi al’ummar Nijeriya taɓarɓarewar harkar tsaro na kan gaba. A shekarun baya, rikice-rikicen da aka fuskanta a tsakanin makiyaya da manoma sun ta’azzara wanda a dalilin rashin magance matsalar ta hanyoyin da suka dace ya haifar da wata masifar ta ‘Satar Shanu’ da wasu miyagun mutane suka duƙufa akai. Daga baya, harkar ta’addanci da satar shanu ta ƙara haifar da wani sabon salo ta’addanci wanda shi ne na “Garkuwa da mutane”.
Garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa ta ƙara janyo taɓarɓarewar sha’anin tsaro a ƙasar nan. ɗalibai, malamai, likitoci, yara da manya babu wanda ‘yan ta’adda suka bari. Abin takaici da ban haushi, sun mayar da garkuwa da mutane kamar wata sana’a ta hanyar karɓar kuɗin fansa. Masu fashin baƙi a kan harkar tsaro sun bayyana yadda waɗannan ‘yan ta’adda suke amfani da kuɗin fansa domin bunƙasa harkokin ta’addancinsu ta hanyar sayen mugayen makamai da miyagun ƙwayoyi.
Wannan garkuwa da ake yi da mutane babu gaira babu dalili ta jefa al’umma da dama cikin tsaka mai wuya. Mutane sun shiga wani yanayi na fargaba da ruɗani kan makomar rayuwarsu da ta iyalansu. Abin tausayi da takaici, a shekarun baya, an taɓa rawaito wani labarin cewa an yi garkuwa da wani matashi a Jihar Katsina, inda masu garkuwar suka nemi kuɗaɗe masu yawa a matsayin kudin fansa.
Mahaifin wannan matashi ba shi da kuɗi kuma ba shi da inda zai nemo kuɗin nan don ya fanshi ɗansa, sai kawai ya yanke shawarar hawa jinkar gidansa domin ya kunce ta, da niyyar sayarwa don haɗa kuɗin fansar. Babu shakka an jefa rayuwar bayin Allah da dama cikin mummunan hali, saboda abubuwan da suke faruwa na ta’addanci da satar mutane.
Abu ne da muka sani ne ga kowa cewa garkuwa da mutane na da illoli masu yawa waɗanda kan kawo rashin cigaba a cikin al’umma. Harwayau, yana jawo yunwa a ƙasa, sakamakon yadda yake hana manoma zuwa gonakinsu domin tsoron kada a yi garkuwa da su, ko kuma a hallaka su. Haka zalika ta kan janyo cikas a harkokin ilmi. A wasu yankunan na karkara da yawa daga cikin iyaye basu barin yaransu su je makaranta domin tsoron masifar da za ta iya biyo baya. Haka kuwa tana janyo durƙushewar zamantakewar mutane a tsakanin junansu. A makon da ta gabata, mun ji yanda ‘yan ta’dda suka yi garkuwa da marigayi Sarkin Gobir. Kuma duk da biyan kuɗin fansa da aka yi wannan bai hana su kashe shi ba, yayin da har yanzu babu wanda ya san inda gawar marigayin take. Babu shakka muna Allah wadai da irin wannan rashin imani! Allah ya jiƙansa ya kuma karɓi shahadarsa.
A shekarar 2019, wani malamin Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina mai suna Dadiyata an sace shi jim kaɗan bayan dawowarsa gida daga wata ziyara da ya kai birnin Kano. Daga wannan lokaci, yau shekara biyar kenan babu labarinsa ko yana raye ko kuma an kashe shi. Iyalinsa da ‘yarsa na cikin wani hali na ƙunci, wanda Allah ne kaɗai ya sani. A wannan shekara ta 2024, wata likita a asibitin ido na Gwamnatin Tarayya da ke Kaduna mai suna Dr. Ganiyat Popoola an kai mata hari gidan ta aka yi garkuwa da ita da mijinta da yara. An sake mijinta bayan kudin fansa da aka biya amma matar har yanzu tana hannun yan ta’dda.
A wannan makon, ƙaramin minista mai kula da sha’anin tsaro ya ɗau alwashin cewa za su fatattaki ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane. Burin kowanne ɗan ƙasar nan shi ne ya ga an kawo ƙarshen wannan ta’addancin garkuwa da mutanen. Da fatan kalaman ministan za su haifar da ɗa mai ido.
A fahimta ta hanyoyin magance matsalar garkuwa da mutane ita ce Gwamnatin Tarayya ta ɗauki ƙwararan matakai wajen kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar nan. Sa’annan ta bai wa jami’an tsaro dukkan a’gajin da suke buƙata wajen murƙushe ‘yan ta’adda. Masu iya magana na cewa ɗan da ya hana mahaifiyarsa bacci shi ma ba zai yi ba. Jami’an tsaro su yi aikin su yadda ya dace babu sani babu sabo, su tabbatar sun murƙushe waɗannan maƙiya zaman lafiyar. Haka kuma, akwai buƙatar al’umma su ma su taimaka wa jami’an tsaron da bayanan sirri da za su taimaka wajen gano maɓoyar ‘yan ta’dda da ayyukan da suke yi. Sa’annan al’umma su guji yaɗa farfaganda, labaran ƙarya marasa tushe, ko kuma yaɗa irin bidiyon da ‘yan ta’adda suke aikawa ta shafukan sada zumunta.
A ƙarshe, gwamnati ta taimaka wajen kuɓutar da Dadiyata da Dakta Ganiyat Popoola da sauran waɗanda suke hannun ‘yan ta’adda.
Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar tsaro ya kuma zaunar da ƙasarmu lafiya. Amin.
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan wannan lambar waya 09059323221
