‘Yan sanda sun kama mutum 18 da ake zargi da satar mutane a Benuwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sanda a jihar Benuwai ta ce jami’anta sun kama wasu mutum 18 da ake zargi da satar mutane tare da ƙwace makamai daga wajensu.

Mai magana da yawun rundunar, Catherine Anene Sewuese, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin da maraice, ta ce mutanen da ake zargin sun yi ƙoƙarin tserewa jami’an ‘yan sanda a wani wajen binciken ababen hawa a kan hanyar ƙaramar hukumar Utonkon inda aka kama su.

Ta ce an samu makamai a wajen mutanen ciki har da bindiga ɗaya samfurin AK-47, da ƙananan bindigogi biyu da kuma alburusai da dama da aka naɗe a jarida.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ta ce tuni aka ƙaddamar da bincike a kan mutanen waɗanda yanzu haka ke hannun ‘yan sanda a tsare.

A ɓangare guda kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ma ta ce ta kama wasu mutum biyu da take zargi da satar mutane da kuma mallakar makamai.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP, Mahid Mu’azu, ya raba wa manema labarai, ya ce mutanen dukkansu daga ƙaramar hukumar Dukku, an kama su ne a kan hanyarsu ta zuwa mavoyar da suke taruwa a dajin Yankari da ke Bauchi.

Ya ce, an kama su ne a ranar 19 ga watan Augusta a ƙauyen Tudun Kwaya da ke ƙaramar hukumar Biiliri tare da haɗin gwiwar jami’an sintiri da mafarauta a yankin.

Ya ce koda aka tambaye su sun bayyana cewa suna daga cikin masu satar mutanen da ke addabar mutane a Pindiga.