Wayar salula ta yi sanadin ƙonewar gidan mai qurmus a Jihar Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar ‘yan kwana-kwana ta Jihar Legas ta ce a ranar Litinin, wani mutum ya sami raunuka bayan da wani abu ya fashe a wani gidan mai mai zaman kansa da ke garin Badagry na jihar.

Babban jami’i da ke kula da reshen hukumar ta Badagry Abel Husu ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN aukuwar wannan iftila’in.

Ya ce hukumar tasu ta sami labarin abin da ke aukuwa ne a gidan man Yemoral Oil and Gas Petrol Station da ke kan hanyar Ajara a Badagry da misalin ƙarfe 8:55 na ranar ta Litinin.

Ya ce jami’ansa sun isa gidan man bayan minti 10 da sami rahoton, kuma nan take suka fara ƙoƙarin kashe gobarar.

“Bincikenmu ya tabbatar cewa wani direban mota ne ya haddasa gobarar, bayan da ya riga ya sayi man fetur a cikin motarsa”.

Ya kuma ce “bayan da mai motar ya tayar da injin motar sai ta yi bindiga, inda gobara ta tashi nan take”.

Sai dai ma’aikata a gidan man sun shaida wa NAN cewa wani mutum ne ya yi sanadin gobarar bayan da ya amsa wayarsa a daidai lokacin da ake zuba ma sa fetur cikin wata jarka.