An dakatar da ɗaukar sababbin ‘yan sanda bayan Sufeto-Janar na Nijeriya ya koka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar da ke kula da batutuwan da suka shafi aikin ɗan sanda a Nijeriya (PSC) ta dakatar da aikin ɗaukar sababbin kuratan ‘yan sanda.

Hukumar ta ɗauki wannan matakin ne ƙasa da sa’a 24 bayan da Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya Usman Baba ya bayyana ɓacin ransa kan wani talla da aka wallafa kan ɗaukar masu sha’awar aikin ɗan sandan.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar, Sufeto-Janar ɗin ya buƙaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da tallar da aka wallafa a wsu manyan jaridun ƙasar.

A nata ɓangaren, hukumar ta PSC ta ce akwai wani rashin fahimta tsakaninta da rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya ce nan ba da daɗewa ba za a sasanta kan wannan batun. Ya kuma ba masu sha’awar aikin da su jinkirta zuwa wani lokaci nan gaba.

Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da masu shirin neman aikin ka da su kuskura su cike bayanansu cikin shafin da kuma kan tashar yanar gizon.

Mista Adejobi ya ce shafin yanar gizon ba shi ne hanyar da za a ɗauki aikin ‘yan sandan ba.

Ya ce fara aikin ɗaukar ma’aikata na shekarar 2022 za a bayyana shi ta hanyar gidan yanar gizon ɗaukar ma’aikata na ‘yan sanda: https://policerecruitment.gov.ng.
Mista Adejobi ya ƙara da cewa za a kuma sanar da jama’a ta shafin intanet na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, https://www.npf.gov.ng.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta PSC ta taba kai karar rundunar ‘yan sandan Najeriyar da tsoho sufeto-janar Mohammed Adamu kan gudanar da aikin ɗaukar kuratan ‘yan sanda 10,000 a 2019, sai dai daga baya sun sasanta.